Tirkashi: An gano wani boyayyan al’amari da yasa ‘yam matan hausawa suke yin bilitin tare da shan kwayoyi da yin allura

Tirkashi: An gano wani boyayyan al'amari da yasa 'yam matan hausawa suke yin bilitin tare da shan kwayoyi da yin allura

Akwai wasu manya-manyan dalilai da suke sa mutane suke sauya launin fatr su daga bakake su koma farare, a cikin wannan labarin zakuji kwararan dalilan da yasa wasu mutanen suke amfani da mayukan kamfani domin sauya launin fatar su daga baka zuwa fara.

Hakika babu mutumin da yake daukar wani mataki a rayuwar sa ba tare da wani kwakkwaran dalilin ba, sabida haka wanda suke amfani da mayukan kamfani domin sauya launin fatar jikin su suma akwai dalilin da yasa suke haka.

Wani lokacin zakuga ana kiran mutum da baki mummuna ko kuma kuji kawan mace suna ce mata wai ke kullum ya kike kara baki ne, wanda kuma masu fada mata hakan zakugam su farare ne dalilin haka suke tsokanar ta.

Ya kamata a matsayin mu na ‘yan Nageriya kasa daya al’umma daya wadanda suke farare su rungumi bakaken fada, sannan kuma su daina amfani da wadannan kalaman domin sukan yi tasiri a zukatan wadanda ake fadawa.

Duk da illolin da bilitin yake haifarwa amma ba’a daina yin sa ba domin a yanzu haka ya karade ko’ina, a wannan zamani duk wani kamfani da yake sanar da mayin bilitin to tabbas yana ciniki sosai.

A kwai wadanda basa iya jurewa a lokacin da ake tsokanar su kan cewa su bakake ne musamman mata, to hakan ne yasa basa iya jurewa sai sun dauki matakin yin bilitin domin suma su koma farare.

Sannan kuma kalaman tsokanar sukan hana mutum kwanciyar hankali don haka ne yasa wasu suke fara shafe-shafen mayukan bilitin.

Yawan maganganun sukan sa wasu su garzaya har zuwa shaguna domin sayan mayukan bilitin din kama daga, sabula, allura, kwayoyi, domin su koma farare kamar sauran abokadan nasu.

Wannan dalilin yasa duk wani kamfani da yake samar da mayukan bilitin ko abubuwan da zasu sa fatar mutum tayi fari, a kullum suke kara samin daukaka da kuma bunkasa a duk kasashen bakar fata.

Karanta wannan labarin.

Mutuwar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din LABARINA Yanzu Akayi Cikakken Bayani Akan Mutuwar Tasa

Karanta wannan labarin.

Subahanallahi: Wata bidiyon Sadiya Haruna mai saida maganin mata ta bayyana wanda ta janyo mata cece-kuce

Karanta wannan labarin.

Yanzu Gaskiya Ta Bayyana Akan Mutanen Da Suke Lalata Rayuwar ‘Yan Arewachin Nigeria

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button