Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun kwace wasu kauyuka a jihar Sokoto tare da nada wasu daga cikin su shuwagabannin kauyukan
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kwace wasu kauyuka a jihar Sokoto tare da nada wasu daga cikin su shuwagabannin kauyukan

Kamar yadda kuka sani ‘yan bindiga suba tawan kaiwa hare-hare kauyuka sannan kuma su lalata dukiyoyin jama’ar kauyen tare da kashewa wasu daga ciki.
A yau kuma mun sami wani labari mai cike da abin mamaki ga ‘yan bindigar, inda suka gudanar da juyin mulki a wasu kauyuka, inda suka nada wasu daga cikin su a matsayin shuwagabanni kauyukan.
Ga cikekken labarin yadda yake.
Dan bindiga Bello Turji da yaran sa sunyi juyin mulki a wasu kauyuka dake karamar hukumar sabo birnin nihar Sokoto.
Yaran Bello Turji da suka hada da, Bakkwalo, Boka I Tamiske, Hassan dan kwaro, Dogo, Jammu baki, sun gayyaci jama’ar da suke kauyen domin tattauawa a kauyen mai suna Suturu a ranar Alhamis data gabata 4/10/2021.
A lokacin da suka yi zaman tattauwar sai suka umarci jama’ar kauyen Gangara da su zabi daya daga cikin ‘yan bindigar mai suna Dan Bakkwalo, a matsayin matsayin sabon hakimin kauyen nasu Gangara.
Nan take sabon hakimin da suka nada dan bindigar mai suna Dan Bakkwalo ya fara basu umarni akan, bude kasuwanni da masallatai da dai sauran su.
A kauyen Makwaruwa daya dan bindigar mai suna Boka Tamiskye ya nata kan sa a matsayin hakimin su inda ya kira taron gaggawa da umartar hakimin garin mai suna Dan Sani.
Daya sanarwa da talakawan sa da kan sa cewa yanzu Boka Tamiske ne sabon hakimin su ba Dan Sani ba.
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Kai Tsaye Tattauna Da Aminu Saira Kan Mutuwar Mahmud A Cikin Shirin Findi Labarina Mai Dogon Zango
Karanta wannan labarin.