Sai shugaba Buhari yayi bayani a gaban Allah kan rashin tsaron dake damun mutanen Arewa, cewar Attahiru Bafarawa

Sai shugaba Buhari yayi bayani a gaban Allah kan rashin tsaron dake damun mutanen Arewa, cewar Attahiru Bafarawa

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto ya bayyana cewa, al’ummar Arewa maso yammacin Nageriya suna cikin bala’in rashin tsaro.

Attashiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa, jama’a basu da damar da zasu kawo kayan gonansu gida a yau, sannan yace ana fama da yunwa an rufe hanyoyin sadarwa da kasuwanni a garuruwa.

Tsohon Gwamnan jigar Sokoto Attarihu Dalhatu Bafarawa ya bukaci Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dage akan matsalar rashin tsaro dake damun kasar Nageriya.

Sannan ya kara da cewa: A halin yanzu yankin Arewa maso yammacin Nageriya yana cikin tashin hankali, ya bayyana hakan ne a lokacin da BBC Hausa tayi shira da shi.

Attahiru Bafarawa ya koka akan halin da al’ummar yankin sa dana shugaban kasar suke ciki, bayan jaridar Vanguard ta bibiyi shirar da aka yi da Attahiru Bafarawa.

Attahiru Bafarawa yace: Sha’anin rashin tsaro wani bala’i ne daya shigo mana mutanen da suke can ne kawai zasu iya bayanin halin da ake ciki a jihar Sokoto da Zamfara.

Ya kara da cewa: Abin takaici ma shine tsaron kasa yana kan wuyan Gwamnatin tarayya masu fadawa shugaba Buhari abubuwan da zasuna tafiya dai-dai, ko suna ce masa da matsala ne?.

Idan suna sanar dashi cewa abubuwa suna tafiya dai-dai ne to sun cuce shi sannan muna sun cuce mu.

Sannan yace: Yau naje gida na dawo na shaida da idanuna ba fadamin aka yi ba, mutane sun noma shinkafa da gero amma sun kasa kaiwa amfamin gida.

Duk wanda yake gona ya dauko kayan noman da yasa mu bazai dawo da rai ba, kamar Zamfara an tsare mutane babu damar yin waya sannan kuma an rufe kasuwa.

Lokacin da ake tambayar Attahiru Bafarawa kan cewa, ko adawa ce tasa yake wadannan maganganun sai yace, lamarin ya shafi har shugaban kasa kuma Allah (SWT) zai tambaye shi.

Karanta wannan labarin.

A wannan talatar ce za’a bude kasuwa a gangara karkashin jagorancin Ɗan Bindiga Hassan ko ya zata kaya da sojojin Nigeria.

Karanta wannan labarin.

Wata Sabuwa Zan Fice Daga Addinin Musulunchi Domin Banga Amfaninsa Ba Cewar Abba

Karanta wannan labarin.

Tsohuwar jarumar kannywood Mansurah Isah ta caccaki shuwagabanni tare da zazzafan martani akan tsadar rayuwa

Karanta wannan labarin.

Wata Sabuwa Zan Fice Daga Addinin Musulunchi Domin Banga Amfaninsa Ba Cewar Abba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button