Trending

Yanzu Aka Bayyana Munanan Abubuwan Dasuka Faru A Kannywood Da Kuma Masu Daɗi Guda Takwas (8) A Satin nan

Yanzu Aka Bayyana Munanan Abubuwan Dasuka Faru A Kannywood Da Kuma Masu Daɗi Guda Takwas (8) A Watannan

Kamar Dai Yadda Kuka Sani Masana’antar Kannywood Na Daya Daga Cikin Masana’antun Da Sukafi Jan Hankalin Mutane Duba Da Yadda Suka Karbu A Nigeria Ciki Da Waje.

A Wani Dogon Bincike Da Akayi Angano Wasu Abubuwa Guda Takwas Dasuka Faru Acikin Watannan Da Kuma Watan Daya Gabata Kamar Yadda Shafin Hausa Legit Ya Rawaito.

1 – Ali Nuhu Bai Taya Adam A Zango Murnar Samun Haihuwa Ba.

Kamar Yadda Kuka Sani Alakar Jaruman Kannywood Tafi Karfine Ta Bangaren Kafafen Sada Zumunta Musamman Shafin Instagram Da Twitter, A Wannan Satin ne Matar Jarumi Adam A Zango Ta Samu Haihuwa, Ma’ana Ta Haifi Yarinya Duk Da Munga Dayawa Daga Cikin Jaruman Masana’antar Suna Wallafa Hoton Jaririyae Tare Da yiwa Adam A Zango Fatan Alkhairi.

Amma Har Yanzu Bamu Ga Ali Nuhu Ya Wallafa Wannan Hoton Jaririyar Ko Kuma Hoton Adam A Zango A Shafinsa Ba, Domin Tayashi Murna Na Samun Karuwar Yaro.


2 – Sabon Film Din Avengers Da Jaruman Kannywood Suke Shiryawa.

Jaruman Hausa sun shirya wani fim da suka sanya wa suna ‘Avengers’ wanda aka shirya shi da yaren turanci, kuma ya kunshi zaratan Jaruman Kannywood.

Shirye-shirye sun yi nisa na fara nuna fim din a gidan kallon Sinima dake Kano Wanda Bature Zambuk Ya Bada Umarni.

3 – Mansurah Isah Ta Koka Kan Halin Da Nigeria Take Ciki A Yanzu

Fitacciyar Jarumar Ta Koka Kan Yadda Abubuwa Suke Faruwa Marasa Dadi, Musamman A Yankin Arewachin Nigeria Wanda Daga Karshe Duk Tsamarin Abun Baya Karewa Akan Kowa Sai Talakata Ga Bidiyon Datayi Cikakken Bayani.

4 – An Karrama Furodusa Usman Uzee A Jami’ar Togo.

Babban Furodusa Usman Uzee Ya Samu Lambar Yabo A Jami’ar Togo Yadda Suka Bashi Shaidar Digiri Na Biyu.

Yadda Muka Ga Abokin Aikinsa Falalu A Dorayi Ya Wallafa Hotonsa A Shafinaa Tare Da Fatam Alkhairi A Gareshi.

5 – Nafisa Abdullahi Ta Bude Shagon Kwalliya.

Fitacciyar Jarumar Film Din Hausa Wanda A Yanzu Take Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Shirin Film Dinann Mai Dogom Zango Wato Nafisat Abdullahi, Ta Bude Shagon Kwalliya Wanda Aka Saka Masa Suna, Nafs Cosmetic’s.

6 – Wasu Jarumai A Kannywood Din Sun Tafi Umrah.

Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun tafi aikin Umrah bayan buɗe Makkah a karon farko tun bayan ɓarkewar cutar COVID19. Daga cikin waɗan da suka je Umrah akwai, Sadiq Sani Sadiq, Aisha Izzar So, Abdul Amart Mai Kwashewa da kuma AS Mai Kwai.


7 – Almajirai Sun Kalli Film Din Fanan Na Mansurah Isah A Cinema.

Jaruma Hadiza Gabon ta ɗauki nauyin Almajirai 40 su kalli sabon fim ɗin ‘Fanan’ a gidan Sinema na Platinun da ke kan hanyar Zaria a Kano.

Mansurah Isah, wacce ta ɗauki nauyin sabon fim ɗin, ita ce ta bayyana haka tare da wallafa hoton tare da yi wa Gabon godiya.

8 – Rahama Mk Jarumar Kannywood Tayi Aure A Ɓoye.

Fitacciyar Jarumar Film Din Hausa Wanda Akafi Sani Da Rahama Mk, Wanda Take Taka Muhimmiyar Rawa Acikim Shirin Film Mai Dogon Zango Wato Kwana Casa’in, Wanda Ta Fito A Matar Gwamna Tayi Aure A Boye Kamar Yadda Rohotanni Suka Bayyana.

Jaruma Rahama MK matar bawa maikada a shirin kwana casa’in tayi auren sirri da ba kowane ya sani ba

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wadannan Abubuwa Dasuka Faru A Masana’antar Kannywood, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbim Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Rahama Sadau Ta Samu Lambar Girma Daga Kamfanin Fina-finan Kudu

Ku Karanta Wannan Labarin:

Mutuwar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din LABARINA Yanzu Akayi Cikakken Bayani Akan Mutuwar Tasa

Ku Karanta Wannan Labarin:

Tsohuwar jarumar kannywood Mansurah Isah ta caccaki shuwagabanni tare da zazzafan martani akan tsadar rayuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button