Ankama wani mutum mai shekara 60 da satar wayoyin hannu guda saba in 70 da kwamfiyotoci masu yawan gaske.

Ankama wani mutum mai shekara 60 da satar wayoyin hannu guda saba in 70 da kwamfiyotoci masu yawan gaske.

Dubun wani mutum mai shekara 60 ta cika inda aka kama shi da wayoyin sata guda 70 kirar Android da kwamfutocin Laptop da sauran abubuwa.

Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC sun kama mutumin ne bisa zargin hada baki wajen fasa gidajen mutane da kuma aikata sata a Jihar Kwara.

Hukumar ta ce tsohon mai suna Bolaji shi ne mai ajiyar kayan da abokin hadin bakin nasa mai suna Shittu wanda ya ƙware wajen fasa gidaje ya shiga ya yi sata — yake sato musu.

Mai magana da yawun hukumar NSCDC a Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya ce dubun tsohon ta cika ne bayan an kama Shittu, wanda shi kuma a wurin bincike ya fallasa alakar da ke tsakaninsu da kuma inda ake ajiyar kayan satan.

Jami’in ya ce hukumar ta kama Shittu ne bayan wata mai suna Yemisi Adefila da ke zaune a unguwar Oko Oba da ke yankin Gaa Akanbi ta kai kara cewa ya fasa gidan iyayenta ya shiga, ya sace musu kayayyaki.

Babawale ya shaida wa manema labaranmu cewa baya ga wayoyi kirar Android guda 70 da kwamfutocin da aka kama a gidan Bolaji, sauran abubuwan da aka gano sun hada da kayan kallo da sauran abubuwa da aka tattara aka tafi da su domin gudanar da bincike a ofishin hukumar.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari na ɓarayin wayoyi a jihar kwara domin jin tabakinku zaku iya biyomu tasahinmu na tsokaci.

KU KARANTA WANNAN:

Da ‘Yam Matan Yanzu Sun San Wadanann Abubuwan Da Rayuwar Aure Baza Tana Lalacewa Ba

Jarumar shirin Dadin kowa Stephanie tayi cikekken bayani akan wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) da tayi jama’a suke cece-kuce

Gaskiyar maganar naɗin masu unguwanni da ƴanbindiga sukeyi yanzu gaskiya ta bayyana.

 

Tirkashi Ashe Har Da Aljannu Acikin Masoyan Ali Nuhu Yanzu Bidiyon Ya Bulla

 

 

Kada kumanta ku danna mana alamar ƙararwar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button