Bayan harin da ƴan bindiga suka kai gida gida sun kashe mutane 11 a wani yanki a jihar katsina.

Bayan harin da ƴan bindiga suka kai gida gida sun kashe mutane 11 a wani yanki a jihar katsina.

Akalla mutum 11 ne ƴan bindiga suka kashe wasu 13 kuma suka jikkata bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai gida-gida wasu yankunan Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

Kakakin Rundunar ƴan Sandan Jihar, SP Gambo Isa ya ce, A ranar Talata da misalin karfe 7:15 na dare, wani gungun ’yan bindiga dauke da bindigun AK-47 sun kai hari kauyukan Katoge da ’Yanturaku na Karamar Hukumar Batsari, inda suka kashe mutum 11, suka jikkata 13.

Tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya tura Mataimakin Kwamishina mai kula da ayyauka na musamman da wasu karin jami’ai zuwa yankin, kuma an tsaurara matakan tsaro inji kakakin.

Dalatopnews ta kuma gano cewa yayin harin, ’yan bindigar sun kona kadarori da yawa a yankunan.

Sun kai hare-haren ne da yammacin ranar Talata, kuma sun shafe kusan sa’a biyu, sannan suka kona gwamman gidaje da gine-ginen gwamnati da motoci.

Shaidun gani da ido sun ce an fara kai harin ne a daren Talata, kuma ’yan bindigar sun kai har kusan farkon safiyar Laraba suna cin karensu ba babbaka.

A dukkan kauyukan da aka kai harin, ’yan bindigar sun rika harbi a iska don ankarar da mutane shigowarsu, kafin su fara bi gida-gida suna satar kayayyaki suna cin zarafin mutane inji majiyar.

Da wakilinmu ya tuntubi mamba mai wakiltar mazabar Batsari a Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Jabir Yauyau, ya ce ya samu labarin kai harin, amma har yanzu yana ci gaba da tattara bayanai a kan hakikanin abin da ya faru.

Sai dai ya ce sakamakon yanke hanyoyin sadarwa a yankin, zai yi wahala a samu cikakkun bayanai yanzu.

An shaida min kai harin da mutanen da aka kashe, galibinsu mutanen da na sani ne, amma duk da haka ina bukatar na kara tantancewa inji dan majalisar.

KU KARANTA WANNAN:

Bani Da Budurwa Amma Nan Da Wata Biyu Zanyi Aure Cewar Presdo Jarumin Film Din Labarina

Ƴan Uwana Ne Suke Zinah Dani Ta Dubura Har Na Haukace Cewar Wata Budurwa

 

Ficaccan mawaki mai tashe a yanzu “Namenj” ya bayyana wani al’amari da yake damun sa a rayuwar sa

 

Me Yasa Mutane Basa Tausayin Baba Dan Audu Ne? Hira Da Rabi’u Rikadawa Kan Cin Zarafin Da Ake Masa

 

Ankama wani mutum mai shekara 60 da satar wayoyin hannu guda saba in 70 da kwamfiyotoci masu yawan gaske.

 

Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button