Ficaccan mawaki mai tashe a yanzu “Namenj” ya bayyana wani al’amari da yake damun sa a rayuwar sa
Ficaccan mawaki mai tashe a yanzu "Namenj" ya bayyana wani al'amari da yake damun sa a rayuwar sa

Ficaccan mawaki wanda yake sharafin sa a wannan lokaci wato “Namenj” ya bayhana wani al’amari da yafu da shi a rayuwarsa wanda yake alshinin hakan.
Ya bayyana wannan al’amarin ne a shafin sa na sada zumunta Instagram a lokacin da yasaki wasu kundin wakokinsa na farko, wanda a cikin kundin a kwai wakoki goma a ciki.
Bayan ya bayyana damuwar tasa sai kuma yayi godiya ga masoyansa da kuma wasu sanannun mutane, wanda suka nuna masa kauna da taimako a rayuwar sa.
Abin da mawaki “Namenj” ya bayyana game da rayuwarsa shine.
Yace abin da yafi damuna shine Mamana ta rasu kafin na sami daukaka kuma nasan addu’ar tace ta kaini inda nake a yanzu, Allah ya jikan mahaifiyata hajiya Fatima da rahama.
Sannan kuma cikin mutanen da suka taimake shi suka nuna masa kauna a rayuwarsa sun hada da, Ali nuhu, Abdaullahi nuhu, Hadiza gabon, MR EAZI, kannywood da dai sauran su.
Sabon kundin wakokin da “Namenj” ya saki mai suna The North Star, wato tauraron Arewa yan nan yana zagaya dumiya.
Karanta wannan labarin.
Me Yasa Mutane Basa Tausayin Baba Dan Audu Ne? Hira Da Rabi’u Rikadawa Kan Cin Zarafin Da Ake Masa
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Da ‘Yam Matan Yanzu Sun San Wadanann Abubuwan Da Rayuwar Aure Baza Tana Lalacewa Ba