Jarumar shirin Dadin kowa Stephanie tayi cikekken bayani akan wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) da tayi jama’a suke cece-kuce
Jarumar shirin Dadin kowa Stephanie tayi cikekken bayani akan wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) da tayi jama'a suke cece-kuce

Jarumar shirin Dadin kowa Sarah Aloysios wacce kowa yafi sanin ta da Stephanie, tayi karin bayani akan akan wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) wanda tayi a kwanakin baya akayi ta cece-kuce a kai.
Tun lokacin da jaruma Stephanie ta bayyana a cikin wata bidiyo wanda tayi shiga irin ta addinin musulinci, sannan take rera wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) inda jama’a da dama sukayi ta tofa albarkacin bakin su a kai.
Wasu daga cikin mutane sunyi zaton ko jarumar tayi hakane domin neman suna a wajan mabiyanta musulmai na shafukan sada zumunta, inda wasu kuma suke zaton jarumar tana sha’awar shiga addinin musulinci ne.
Jaruma Stephanie tayi karin bayani akan wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) da tayi a cikin wata bidiyo, da zaku kalla a kasa.
Kai musulmi ni kirista ce ban tashi na roki Allah don yayi ni a kirista ba, haka zalika kai ma musulmi ba ka tashi ka roki Allah yayi ka a musulmi ba.
Jaruma Stephanie da cewa, kawai wayar gari kowa ya yi ya gan shi da addinin sa, Tace tana matukar jin takaici idan taga musulmi ko kirista ya na zagin wanda su ke da bambancin addini da shi.
Ta kara da cewa kowa nata ne kuma duk wanda zai so ta yaso ta yadda ta ke.
Ga bidiyon nan dokin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin jaruma Stephanie.
https://www.facebook.com/voahausa/videos/348411227088211/?app=fbl
Karanta wannan labarin.
Gaskiyar maganar naɗin masu unguwanni da ƴanbindiga sukeyi yanzu gaskiya ta bayyana.
Karanta wannan labarin.
Tirkashi Ashe Har Da Aljannu Acikin Masoyan Ali Nuhu Yanzu Bidiyon Ya Bulla
Karanta wannan labarin.
Inna lillahi wainna ilaihir rajiun ansami mummunan hatsarin mota