Tirkashi wani ɗan bindiga ya tona asirin wasu ƴan siyasa a jihar Sokwato wanda dasa hannunsu a yin ta addancin Jihar.

Tirkashi wani ɗan bindiga ya tona asirin wasu ƴan siyasa a jihar Sokwato wanda dasa hannunsu a yin ta addancin Jihar.

Wani dan bindiga da ya shiga hannu a Jihar Sakkwato ya fallasa iyayen gidansu a cikin manyan yan siyasar jihar baki ɗaya.

Kwamandan Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Sakkwato Saleh Dada, ya tabbatar wa Kamfanin Daillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa dan bindigar mai suna Danlabbo ya shaida musu cewa shi makusancin wasu manyan ’yan siyasa ne kuma su ne suka sanya shi a harkar ’yan bindiga.

Dan labbo ya yi wannan fallasa ne bayan Hukumar ta kama shi da wasu yan bindiga da masu kai musu bayanai hudu a yankunan jihohin Sakkwato da Zamfara.

Kwamandan ya ce tuni suka fara gayyato dan siyasan da Danlabbo ya ambaci sunansa domin amsa tambayoyi a ofishin hukumar. Sai dai bai bayyana wa majiyarmu sunan dan siyasar ba.

Da yake gabatar da su a ranar Laraba, Kwamandan hukumar ya ce daya daga cikin yan bindigar da dubunsu ta cika kuma ya tabbatar musu cewa ya kashe mutane da dama a hare-haren da suka kai.

Sun kuma tabbatar wa hukumar cewa da su ake yin garkuwa da wasu manyan mutane, satar dabbobi da kashe-kashe da sauran ayyukan ta’addanci a kauyukan jihohin Sakkwato da Zamfara.

Ya ce mutanen da aka kama

yanasalin yankunan Tureta da Dange-Shuni ne a Jihar Sakkwato, kuma shekarunsu 27 ne zuwa 48.

KU KARANTA WANNAN:

Yanzu Maryam Yahaya Ta Sake Sakin Bidiyonta Na Sharholiya A Shafin Tiktok Cikin Nishadi

Gara masu Luwadi da masu yin Maulidi Sheikh Anas Taufiq yayi karin bayani akan abin daya fada

Jaruma Hadiza gabon tare da Dan kwallon kafa na Nageriya Shehu Abdullahi sun bayyana wani al’amari akan mutuwar Mahmud a shirin Labarina

Mutum 107 da a ka kama suna karɓar horan soja a wani sansanin sojoji na bogi.

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button