Trending

An Gurfanar Da Hafsat Idris Gaban Kotu Saboda Ta Cinye Kudin Aiki Jarumar Kannywood

An Gurfanar Da Hafsat Idris Gaban Kotu Saboda Ta Cinye Kudin Aiki

Kamar Yadda Kuka Sani A Kwanakin Baya Antattauna Batun Karar Hafsat idris Barauniya Akan Cinye Kudin Aikin Wani Kamfani Da Tayi, Yadda Har Akaso Ayi Shari’ar Amma Daga Baya Aka Daga Shari’ar.

Babbar kotun jiha mai lamba 18, da ke
zamanta a garin Ungoggo, karkashin mai
shari’a Zuwaira Yusuf, ta ci gaba da shari’ar jarumar masana’atar shirya Fina-finan Hausa ta Kannywood Hafsat Idris, da wani kamfani UK Entertaiment, kan zargin kin karasa musuaiki.

Wakilin Dala fm Abubakar Sabo ya rayaito
cewar, Kamfanin ya na karar Hafsat Idris ne, akan Sunyi jinga da ita A Wani Kamfanin TV Show, na Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Uku, sai dai kafin a karasa aikin ta gudu.

Acikin Rohoton Da Ma’aikacin Dala FM Kano Ya Bayyana, Kamfanin Ya Kawo Karar Jarumar Ne Domin Ta Biyasu Kudinsu Na Aiki Naira Miliyan Daya Da Dubu Dari Uku, Sanann Kuma Ta Biyasu Kudin Hasarar Da Sukayi Na Kayan Aiki Naira Miliyan Goma, Saboda Sanadiyya Guduwar Datayi Kafin A Fara Shirin Yayi Silar Lalacewar Wasu Kayan Aikin.

Kamfanin Da Lauyoyinsa Sun Tsaya Kan Dole Sai Jarumar Ta Biya Zunzurutun Kudin Nan Wanda Jimillarsa Yake Dai-dai Da Naira Miliyan Sha Daya Da Dubu Dari Uku, Wanda Ake Tuhumar Jarumar Da Sai Ta Biya Tunda Bata Yi Aikin Da Aka Bata Ba.

Ga Bidiyon Sai Ku Kala Kuji Cikakken Bayani Daga Bakin Ma’aikacin Gidan Radion Dala FM Din Akan Karar Hafsat Idris.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinmu A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wanann Al’amari Na Kama Jaruma Hafsat Idris Da Cinye Kudin Aiki, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Mana Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryyenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Yanzu Maryam Yahaya Ta Sake Sakin Bidiyonta Na Sharholiya A Shafin Tiktok Cikin Nishadi

Ku karanta Wannan Labarin:

Yanzu Wani Sabon Bidiyon Maryam Yahaya Ya Bulla Na Sharholiya A Shafin Tiktok Bayan Rashin Lafiya

Ku karanta Wannan Labarin:

Yanzu Hadiza Gabon Ta Bayyana Abubuwa Marasa Dadi Da Kuma Kalubalen Data Fuskanta A Rayuwarta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button