Fulani sun nuna rashin jin daɗinsu akan lugudan wutar da sojoji sukayiwa sha nunsu.
Fulani sun nuna rashin jin daɗinsu akan lugudan wutar da sojoji sukayiwa sha nunsu.

Jiragen sojoji sun hallaka shanu 1,500 bayan sun yi musu luguden wuta a wasu kauyukan Fulani da ke Karamar Hukumar Takum a Jihar Taraba.
Jiragen sojojin sun yi wannan luguden wuta ne a yankunan Kashinbila da Tor Donga a ranakun Laraba da Alhamis.
Wani makiyayi a yankin Sadu Saidu ya ce daya daga cikin jiragen ya kashe masa shanu 120 da shanun dan uwansa 105 a harin.
Muna shirin fita da dabbobinmu zuwa kiwo sai muki ji karar jirgin da zuwansa kafin kiftawa da Bismillah sai ya bude wuta.
Nan take muka arce muka shige cikin daji muka labe don tsira da rayukanmu Cikin dan kankanin lokaci da aka yi abin na farko sai da muka kirga shanu kusan 700 da aka kashe inji Sadu.
Ya ce washegari wani jirgi ya sake kai hari a wasu kauyukan Fulani inda a nan kuma ya kashe shanu 750.
Shi ma wani Bafulatani a yankin mai suna Musa ya ce bayan shanun da aka kashe akwai shanu da dama da suka samu raunin harbi dole suka je aka yi gwanjonsu a kasuwar garin Takum kafin su kasa.
Musa wanda ya ce daruruwan Fulani sun fara kaura zuwa yankin kasar Kamaru da garken shanunsu, ya kara da cewa bayan harin sai da naman shanu ya bazu a kasuwar Takum, wanda dole ake sayarwa da arha saboda yawansa.
Mun yi kokarin jin ta bakin Shugaban kungiyar Fulani ta Miyyetti Allah a Karamar Hukumar Takum Alhaji Bello amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.
Mun yi ta kiran wayarsa amma bai amsa ba har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto.
Kakakin Rundunar Yan Sanda ta Jihar Taraba DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da harin jiragen yakin amma ya ce a Jihar Binuwai abin ya faru ba Jihar Taraba ba.
Shedar gani da ido yatabbatar mana dacewa duk wanda ya faɗi adadin wanda suka mutu ƙaryane.
Tabbas Wadannan Ne Abubuwan Dasuke Lalata Rayuwar Auren Hausawa Guda (60)
Tofa Rundunar ƴansandan jihar Enugu sun kama wani mutum bisa Zarginsa da saida ɗansa.
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.