Jami’an ‘yan sanda sunyi raga-raga da wani mai garkuwa da mutane lokacin da aka kama shi yake kokarin tserewa
Jami'an 'yan sanda sunyi raga-raga da wani mai garkuwa da mutane lokacin da aka kama shi yake kokarin tserewa

Jami’an tsaron ‘yan sanda sun sami nasarar harbe wani mai garkuwa da mutane lokacin da yake kokarin guduwa, sannan kuma ‘yan sandan sun kama guda hudu daga cikin wasu garkuwa da mutanen.
Kwamashinan ‘yan sandan jihar Niger, Mista Monday Kuryas yace, maharan sun yi garkuwa da wasu mutane guda biyu a ranar Alhamis, sannan kuma shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kara da cewa: Tuni aka tura jami’an da suke yaki da masu garkuwa da mutane domin su ceto mutanen da aka yi garkuwar da su.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis 11 ga watan Nuwanba inda aka kama wasu mutane guda hudu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Niger, Mista Monday Kuryas, ya sanar da kamfanin dillancin labarai ba Nageriya a garin Minna babban birnin jihar inda yake cewa, wadanda ake zargin sunyi garkuwa da mutane biyu a ranar Alhamis.
Mista Monday Kuryas ya kara da cewa: An tura tawagan ‘yan sanda wanda suke yaki da masu garkuwa da mutane da ‘yan banga domin su ceto mutanen da aka sace.
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
An Gurfanar Da Hafsat Idris Gaban Kotu Saboda Ta Cinye Kudin Aiki Jarumar Kannywood
Karanta wannan labarin.