Shedar gani da ido yatabbatar mana dacewa duk wanda ya faɗi adadin wanda suka mutu ƙaryane.

Shedar gani da ido yatabbatar mana dacewa duk wanda ya faɗi adadin wanda suka mutu ƙaryane.

Yan Najeriya 13 da ’yan Jamhuriyar Nijar biyar ne hukumomi suka tabbatar da rasuwarsu bayan wata rijiyar hakar zinare ta rufta a kansu a Jamhuriyar Nijar.

Idan baku mantaba a ɗazune muka kawo muku saban rahoto a shafinmu na Dalatopnews namutanan da suka mutu a wajan tonan zinare.

Gawani cikakken bayani daga wajan shedu da ido.

Wani dan Najeriya mai suna Abubakar daga Jihar Zamfara wanda dan uwansa ya rasu a iftila’in ya ce abin ya faru ne mako biyu da zuwansu neman arzikinsu a yankin amma zuwa lokacin iyayensu ba su san da rasuwar dan uwan nasa ba.

Ina da yan uwa cikin wadanda Allah Ya yi wa cikawa yanzu dai na ga biyu kuma akwai saura a kasa Gaskiya duk wanda ya ce ga adadin wadanda ke karkashin kasar nan ya fada ne dai kawai, jiya dai an fito da mutum 17,” kamar yadda wani ya shaida wa manema labarai wanda ya ziyarci wurin domin gane wa kansa.

Wani mai hakar zinare a wajen ya ce Ana sa ran akwai mutane ba daya ba, ba biyu ba a karkashin kasa saboda duk wadanda ke rijiyar suna kasa abin ya faru ba a ciro su ba Wadanda ke amsar kaya na waje ne aka fiddo su.

Magajin Garin yankin, Malam Adamu Girau yace Abu na al’ajabi ya faru inda wadannan rijiyoyi suka fada gaba daya kuma suka rufta da mutane rayukan mutane da yawa suka rasu; Akalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu.

KU KARANTA WANNAN:

Tofa Rundunar ƴansandan jihar Enugu sun kama wani mutum bisa Zarginsa da saida ɗansa.

Jami’an ‘yan sanda sunyi raga-raga da wani mai garkuwa da mutane lokacin da aka kama shi yake kokarin tserewa

Inna lillahi wainna ilaihir raji’un Allah yayiwa wasu mutane sha uku 13 rasuwa a jihar maraɗi a ramin tonan zinare.

 

Yadda Aka Hadawa Hanah Buhari Bikin Murna Graduation Tare Da Murna Zagayowar Shekararta Da Haihuwa

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button