Darakta Aminu Saira ya bayyana dalilin da yasa aka cire Mahmud daga shirin Labarina mai dogon zango

Darakta Aminu Saira ya bayyana dalilin da yasa aka cire Mahmud daga shirin Labarina mai dogon zango

Kamar yadda kuka sani shirin Labarina mai dogon zango shiri ne wanda yake nishadintar da jama’a masu kallon tare da jan hankalin su duba da abubuwan da suke faruwa a cikin shirin.

Sanin kowa ne a satin da yagata Mahmud ya mutu a cikin shirin Labarina inda kowa yake tunanin mutuwar da Mahmud yayi ba da gaske bane mafarki ne.

Inda akayi da cece-kuce tare da maganganu kala-kala domin jama’a masu kallon shirin suna tunanin idan aka ce Mahmud ya mutu a shirin Labarina, tofa suma ganin kamar shirin zai iya samin nakasu duba da taka rawar ganin da Mahmud yake a cikin shirin.

Har ma aka sami damar tattaunawa da Ficaccan Daraktan shirin Labarina Malam Aminu Saira, inda aka masa tambayoyi akan gaskiyar magana game da mutuwar Mahmud a cikin shirin Labarina.

Amma Darakta Aminu Saira bai sanar da su gaskiyar al’amari ba inda yake musu nuni da cewa, a dakaci shirin na satin gaba domin a lokacin kowa zai san mutuwar Mahmud da gaske ne ko kuma mafarki ne.

To a yau kuma mun sami wani faifai bidiyo daga wata tashar dake kan manhajar Youtube mai suna “Gaskiya24 Tv” inda a cikin bidiyon aka yi shira da Ficaccan Daraktan na shirin Labarina wato Aminu Saira.

Inda aka tattauna da Darakta Aminu Saira akan wani dalili ne yasa aka cire Mahmud daga cikin shirin Labarina, domin kun san dama Mahmud ya mutu a cikin shirin Labarina.

A shirar da aka yi da Darakta Aminu Saira ya musu cikekken bayani akan dalilin da yasa haka ta faru aka cire Mahmud daga shirin Labarina, kamar yadda zaku shirar tasu yadda ta kasance.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekkiyar shirar da aka yi da Daraktan shirin Labarina Malam Aminu Saira.

Karanta wannan labarin.

Malam isah Ali Pantami Bai Kamata Ya Zama Furofesa Ba Cewar Kungiyar Malaman Jami’un Nigeria ASUU

Karanta wannan labarin.

A safiyar yau Asabar rundunar sojojin Nigeria sukayi batakashi da yin ƙungiyar (ISWAP) a jihar Borno wanda ƴan ƙungiyar suka sha da ƙyar.

Karanta wannan labarin.

Tirkashi: Kungiyar Tijjaniyya da Kungiyar Izala zasu hada ka amma bisa wasu sharuda guda uku, inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button