Advertisement
Trending

Duk Rintsi Kada Ku Bari ‘Yan Sanda Su Duba Muku Aljihu Idan Bada Shaidar Kotu Ba – Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Sanarwa

Duk Rintsi Kada Ku Bari 'Yan Sanda Ya Duba Muku Aljihu Idan Bada Shaidar Kotu Ba - Hukumar 'Yan Sanda Tayi Sanarwa

Kamar Yadda Kuka Sani A Tsarin Doka Ne Hukuma Ko Kuma Muce ‘Yan Sanda Suyi Bincike Akan Abubuwan Dasuke Faruwa A Kasa Domin Gudun Aikin Ta’addanchi.

Akwai Matakai Da Dama Da ‘Yan Sanda Suke Bi Domin Ganin Sun Binciki Mutum Walau Ta Zahiri Ko Kuma Badini,Yadda Wani Lokacin Baza’a Baka Damar Ka Shiga Wani Kebantaccen Waje Ba, Face An Chajeka An Duna Aljihunka Saboda Gudun Matsala.

Shafin Northern Vine Na Instagram Ya Bayyana Wani Sako Da Hukumar ‘Yan Sanda Ta Nigeria Ta Fitar Akan Chajen Da ‘Yan Sanda Sukeyiwa Mutane, Wajen Saka Musu Hannu A Aljihu Ga Yadda Rohoton Yake.

northern_vine Duk Rintsi, Kada Ku Bar Yan Sanda Su
Bincika Wayarku Ba Tare Da Samun Umurnin Kotu Ba – Hukumar Yan Sanda

Mataimakin kwamishinan yan sanda, Bassey Ewah yaja hankalin yan Najeriya dangane
da yanda jamian yan sanda suke bincikan wayan matafiya akan hanya.

Mataimakin ya ja hankalin yan Najeriya da su daina barin yan sanda su na binciken wayansu a checking point ba tare da samun urmurni daga kotu ba.

A fadinsa,”Babu wani dan sandan da ya ke da hurumin tareku a hanya ya tambayi wayanku don bincike ba tare da samun umurni daga kotu ba.

Saidai daman kai din ana kan bincikenka ne”.Dadin dadawa, Mr Ewah wanda ya zanta a wani taro na hadin kan yan sanda da mazauna gari da helkwatan yan sandan Jihar Lagos ta shirya, ya kara hasken cewa, matakin da kawai dan sanda zai iya
binciken waya shi ne, idan mutum daman shi mai laifine da ake bincikensa.

A cewarsa “Duk rintsi, kada ku ba kowanne dan sanda wayarku ya yi bincike a yayin da aka tsareku a
checking point” ya jaddada cewa,”Mu yan sanda
bamu da wannan hurumin.

Idan bincikenka mukeyi, za mu gabatar maka da shaida daga kotu sa’annan
mu bukaci ka ba mu wayan naka mu bincika”.

Wannan Shine Rohoton Da Hukumar ‘Yan Sanda Ta Fitar Wajen Chajen Da Akeyiwa Mutane, Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Rohoto, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Tirkashi Ashe Wannan Ne Dalilin Dayasa Wasu ‘Yam matan Suke Zuwa Karuwanchi Suƙiyin Aure

Ku Karanta Wannan Labarin:

Gaskiya Ta Bayyana Akan Daukan Hoton Da Hadiza Gabon Tayi Da Malam Isah Ali Pantami

Ku Karanta Wannan Labarin:

Sai bayan na aure ta na gano ashe Nono daya gareta iyayan matata sun yaudare ni, cewar mutumin daya auri mace mai Nono daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button