Tirkashi: Kungiyar Tijjaniyya da Kungiyar Izala zasu hada ka amma bisa wasu sharuda guda uku, inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tirkashi: Kungiyar Tijjaniyya da Kungiyar Izala zasu hada ka amma bisa wasu sharuda guda uku, inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi

‘Yan Tijjaniyya da ‘Yan Izala zasu kasance a tafiya daya amma akan wasu sharuda guda uku da babban Malamin addini Sheikh Dashiru Usman Bauchi ya gindaya.

Babban Malami kuma jagora a Darikar Tijjaniyya Sheikh Dashiru Usman Bauchi yayi wata magana data janyo cece-kuce sosai, inda yace zasu hada kai da ‘Yan Izala amma ya kafa wasu sharuda guda uku cewa, sai ‘Yan Izala sun cika su sannan hadin kan zai samu.

To sanin kowa nai dai cewa, Darikar Tijjaniyya da Izala dukan su Musulmai ne da suka sami gagarimin sabanin fashimtar juna a tsakanin su, inda kungiyoyin biyu suka raba gari akan abubuwa da dama da suka shafi addini na Musulinci.

Kuma magi girman sabanin da wadannan kungiyoyi guda biyu suka samu a tsakanin su shine Maulidi, sabida kusan shine abin da aka fi magana a kai.

Sai dai a dunkule abin da yaraga wadannan kungiyoyi guda biyu shine bidi’a wato aikata wani abu a cikin addini, wanda Annabi Muhammad S.A.W da sahabban sa musammam khalifofin sa basu aikata ba.

To shikuma Maulidi yana daya daga cikin abubuwan da Annabi Muhammad S.A.W da sahabban sa basu aikata ba, inda ‘Yan Izala suke ganin tun da abin haka ne suma bazasu aikata ba.

Wannan labarin mun same shi a cikin wata bidiyo wanda Tashar Kundin shahara ta wallafa, zaku iya kallon bidiyon domin kuji cikekken labari akan muhawarar da ake tsakanin kungiyar Izala da kungiyar Tijjaniyya.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Karanta wannan labarin.

Tirkashi Ashe Wannan Ne Dalilin Dayasa Wasu ‘Yam matan Suke Zuwa Karuwanchi Suƙiyin Aure

Karanta wannan labarin.

Bidiyan Najlat Muhammad Da Angonta Dan Kwallon Kafar Nijeriya Shehu Abdullahi Tun Bayan Aurensu

Karanta wannan labarin.

Gaskiya Ta Bayyana Akan Daukan Hoton Da Hadiza Gabon Tayi Da Malam Isah Ali Pantami

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button