An kashe malaman makaranta 3,795 tare da kone makarantu akalla 1,500 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
an kashe malaman makaranta 3,795 tare da kone makarantu akalla 1,500 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Cikin tsawon shekara 12 da aka yi ana fama da rikicin Boko Haram, an kashe malaman makaranta 3,795 tare da kone makarantu akalla 1,500 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Babban Manajan Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) Alhaji Mohammed Alkali ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da taron kara wa juna sani na kwana biyar ga malamai 300 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Sa Kashim da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno.
A cewarsa harkokin ilimi sun samu koma baya matuka sanadiyar rikicin wanda hakan ya sa ya zama tilas a rika shirya irin wannan bita don sake inganta harkokin koyo da koyarwa.
Ya kara da cewa sanin kowa ne faruwar wannan rikici ya yi matukar kawo koma baya a harkokin ilimin yankin Arewa maso Gabas duba da yadda aka samu yara da yawa sun kauracewa makarantunsu sun koma gararanba a kan tituna tare da fadawa muggan dabi’u.
Kan abin da ya shafi horar da malaman kuwa Muhammad Alkali ya jaddada cewa akalla malaman makaranta kimanin 1,500 ne za a horar a cikin jihohi 5 a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban kamfanin kwararru na Limo Holdings Consult Lawan Alhaji ya bayyana cewa malaman makarantun firamare da kananan makarantun sakandare ne za a horar.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan wannan lamari na Boko Haram bisa lalata karatun yara don jin tabakinku zaku iya biyo mu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Manya Yayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Wajen Bikin Dan Gwamnan Jihar Jigawa Abdurrahman
Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatarwa mungode.