Manoman Jihar Borno sun fara biyan haraji ga kungiyar ISWAP.

Manoman Jihar Borno sun fara biyan haraji ga kungiyar ISWAP.

Manoma da mazauna a garin Damboa da ke Jihar Borno sun fara biyan haraji ga kungiyar nan mai ikirarin jihadi a Yammacin Afirka ta ISWAP.

Wani babban jami’in gwamnati ya shaida wa wakilinmu cewa a halin yanzu manoma na rayuwa karkashin  jagorancin mayakan ISWAP a yankin Damboa kamar yadda muka kawo mu rahotan a makonnin da suka gabata.

Mayakan sun bai wa mazauna damar noma gonakinsu sannan su rika karbar haraji a matsayin zakka daga kowane manomi bayan sun girbe amfaninsu.

Wasu manoman yankin sun bayyana cewa manoman sun karbi wannan lamari hannu biyu domin sauki ne a garesu.

A lokacin da kungiyar Boko Haram ke karkashin jagorancin marigayi Abubakar Shekau ba su ko barin mazauna su fita gonakinsu amma bayan ISWAP ta yi juyin mulki ta bai wa mazauna damar fita gonaki amma da sharadin tilasta musu biyan haraji.

Wani manomi mai suna Musa Mrusha ya shaida wa wakilinmu na Dalatopnews cewa da yawa daga cikin manoma ya musu tirjiy wanda suka tafi dashi basu san halin da ake ciki.

A lokutan baya, mayakan Boko Haram da dama sun kashe manoma masu tarin yawa a lokacin girbin amfanin gona a irin wannan lokaci.

Amma babu wanda ya samu labarin faruwar irin haka a bana.

KU KARANTA WANNAN:

Bayan harin da ƴan ta’adda suka kaiwa jirgin ƙasar dake sufuri zuwa Abuja Kaduna mutane sunƙi sakin jiki da jirgin dangujewa masu garkuwa da mutane.

 

Yadda Aka Hukunta Saurayi Da Budurwa Bayan Sunyi Zinah A Gaban Mutane Bakin Titi

 

Tirkashi: An bayyana wani sabon al’amri akan jarumi Adam a zango akan auri sakin da yake

Mayaƙan ISWAP da suka kashe Janar Dzarma Zirkusu Sunga ta kansu a wajan sojojin Nigeria.

 

Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button