A ranar Litinin mutum 12 aka kashe a Illela yayin da kuma ragowar ukun suka rasa rayukansu a Goronyo a jihar Sokoto.
A ranar Litinin mutum 12 aka kashe a Illela yayin da kuma ragowar ukun suka rasa rayukansu a Goronyo a jihar Sokoto.

Kimanin mutum 15 ne ake fargabar sun mutu a wani hari na ranar Lahadi da ƴan bindiga suka kai Kananan Hukumomi Goronyo da Illela na Jihar Sakkwato.
Gwamnan Jihar Aminu Waziri Tambuwal wanda ya tabbatar da hakan a ranar Litinin ya ce mutum 12 aka kashe a Illela yayin da kuma ragowar ukun suka rasa rayukansu a Goronyo.
Gwamna Tambuwal ya bayyana mana haka ne jim kaɗan gabanin gabatar da Kasafin Kudin Jihar Sakkwato na shekarar 2022 a gaban Majalisar Dokokin jihar.
Tambuwal hare-haren sun auku ne a tsakanin daren Lahadi zuwa wayewar gari na Litinin a Kananan Hukumomin da lamarin ya shafa.
Gwamnan ya kuma mika ta’aziyyarsa ga ƴan uwan wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata a hare-haren da ƴan bindiga suka kai.
Bayanai sun ce Kananan Hukumomin biyu da lamarin ya shafa na daga cikin wadanda gwamnati ta bayar da umarnin katse musu layukan sadarwa a yunkurinta na kawo karshen matsalar tsaro a Jihar.
Duk wannan dai na faruwa ne a yayin da wasu rahotanni ke cewa ƴan bindiga sun fara daula a kauyuka da dama na Jihar Sakkwato inda har sun shata wa mazauna haraji da zasu dinga biya duk bayan wani lokaci.
KU KARANTA WANNAN:
Tofa In Baba Dan Audu Ne Babanka Wane Mataki Zaka Dauka Akansa ?, A Matsayinka Na Mai Hankali
Bidiyan Gwamna Bala Muhamned Tare Da Yarsa Suna Rawa A Bikin Ta
Wani al’amari ya bayyana akan wasu jaruman kannywood wanda suka sauya kamanni bayan wasu shekaru
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.