Trending

Bayan Hira Da Nuhu Abdullahi, Wanu Saurayi Ya Tona Masa Asiri Yadda Ya Karyata Abunda Ya Fada Acikin Hirar

Bayan Hira Da Nuhu Abdullahi, Wanu Saurayi Ya Tona Masa Asiri Yadda Ya Karyata Abunda Ya Fada Acikin Hirar

A Wani Dogon Sako Da Mukaci Karo Dashi A Shafin Facebook Na Wani Matashi, Wanda Ya Aikewa Da Nuhu Abdullahi Sakon Gaisuwa Da Kuma Cin Gyara Ko Kuma Muce Korafi, Bayan Hirar Da Akayi Dashi Yadda Ya Bayyana Tarihin Rayuwarsa.

Kamar Yadda Kuka Sani Dai A Satin Daya Gabata Ne Akayi Hira Da Jarumin Film Dinnan Wato Nuhu Abdullahi, Wanda Yake Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Shirin Film Dinnan Mai Dogon Zango Wato Labarina.

Jarumin Ya Bayyana Tarihin Rayuwarsa Da Kuma Wasu Abubuwa Da Bakowane Yasani Ba Game Dashi, Yadda Abun Ya Kayatarda Jama’a Sosai.

Sai Dai Bayan Wannan Hira Da Akayi Da Jarumin, Ansamu Wani Saurayi Yayi Wami Korafi Bayan Fitar Wannan Bidiyon Hira Da Nuhu Abdullahi, Yadda Bayaninsa Ya Fara Kamar Haka.
ZUWA GA JARUMI NUHU ABDULLAHI(Mahmud a shirin labarina)

DaGa lshaka Usman Wali

Nayi matukar mamaki irin yadda na kalli
hirarka da BBC HAUSA a shirinsu na
DAGA BAKIN MAI ITA inda sukaso suji
tarihinka.

Kaikuma saika nuna musu cewa anhaifeka a garin kano kayi primary da secondary duk a jihar kano.

Hakika naji babu dadi sakamakon irin yadda naga LA juyawa kauyenku baya saboda yanzu rayuwarka taci gaba kuma nayi mamaki matuka.

Inaso wadanda suka kalli shirin Susancewa an haifi NUHU ABDULLAHI Awani kauye da ake kira tudun bichi akaramar hukumar danko wasagu jihar kebbi.

Nuhu yayi model primary school a tudun bichi inda ya zarce izuwa garin wasagu domin shiga makarantar secondary school
maisuna GOVERNMENT ARABIC ANDISLAMIC SECONDARY WASAGU a lokacin marigayi malam jafaru yana principal inda malam abubakar na diri yake mataimaki.Nuhu abdullahi shine house captain a
wasagu house inda shikuma abokinsa
maisuna habibu random yake house
captain a sakaba house.

Nasanshi yasanni domin kaninsa Aliyu Abdullahi abokinane kuma munyi kwana daki daya dashi nuhu abdullahi.

Lokacinda ina sabon shiga makarantar
akwai wani prefect maisuna Tijani A
Garba kanin matar yayana ne shine
wanda ya daukeni yakaini prefect room
na ringa kwana acan dukda ba house
dina bane domin ni ina danko house newanda Nura yake jagoranta.

Nuhu Abdullahi yasha aikina na debo
masa ruwa a bokiti idan zaiyi wanka
dasauran dawainiya dayake sakani
sakamakon nine yaro kuma junior a
dakin dalilin dayasa bansha watawahalaba kenan saboda mun shakudaduk wani prefect a makarantar.

Bayan anyi shirin gina masallacine Nuhu
yadan sami sabanin fahimta da Malam
abubakar na diri vice principal wanda
shine yayi sanadiyar barinsa makarantar
a lokacinda yake gab da rubuta junior
waec inda yakoma lagos dazama gurin
yayansa maisuna Abdulrahman wanda
shine yayi sanadiyar shigarsa sanaar film acan ne yaci gabada karatu har Allah yataimakeshi ya kammala jami’a.

Duk rintsi da irin niimar dakake ciki baikamata kacire sunan mahaifarka A shafin tarihin rayuwarkaba domin koba komai wadannan yan uwan naka sune sukeyi
maka adduar da fatar alkhairi kuma sunesuke alfaharin cewa dan uwansu yasamu daukaka.

Dafatar Allah yabaka ikon sanin hakkin
mahaifarka Amen.

Tofah Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Game Da Furuchin Wannan Matashi, Yadda Ya Bayar Da Tarihin Nuhu Abdullahi, Sannan Kada Ku Manta Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Masoyan Jarumin Wato Nuhu Abdullahi Domin Yasan Halin Da Ake ciki.

Kada Ku Manta Idan Wannan Shine Farkon Shigowarka Wannan Shafi Munaso Ka Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Bayan Mutuwar Mahaifina, Mun Shiga Tashin Hankali Ni Da Mahaifiyata Cewar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din Labarina

Ku Karanta Wannan Labarin:

Bani Da Budurwa Amma Nan Da Wata Biyu Zanyi Aure Cewar Presdo Jarumin Film Din Labarina

Ku Karanta Wannan Labarin:

Me Yasa Mutane Basa Tausayin Baba Dan Audu Ne? Hira Da Rabi’u Rikadawa Kan Cin Zarafin Da Ake Masa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button