Tirkashi Ankama wanin mutumin Amurka da laifin Karyar Ya Mutu Don Ya Cinye Bashin Naira Miliyan 223
Tirkashi Ankama wanin mutumin Amurka da laifin Karyar Ya Mutu Don Ya Cinye Bashin Naira Miliyan 223

An yanke wa wani mutumin Jihar Massachusetts da ke Amurka hukuncin dauri bayan ya yi yunkurin yin zamba a karkashin shirin tallafin kasuwanci na COVID-19.
Mutumin ya yi karyar cewa ya mutu don guje wa hukumomin kasar kan tallafin bashin da aka ba shi. An dai yanke masa hukuncin daurin wata 56 ne a gidan yari.
Wanda ya aikata laifin mai suna David Staveley ya yi ikirarin cewa ya mallaki manyan kamfanoni hudu inda ya bukaci Dala dubu 544,(kimanin Naira miliyan 223 da dubu 350) a matsayin tallafi daga gwamnatin kasar.
Bayan da aka tuhume shi a bara, Staveley ya yi karyar ya mutu kuma ya yi amfani da bayanan karya ta hanyar satar lasisin lambar mota.
Shi ne mutum na farko da aka tuhume shi da laifin zamba kuma yana bukatar tallafi.
Masu gabatar da kara sun yi Allah wadai da matakin nasa a cikin sanarwar yanke hukuncin.
Ya yi tunanin amfani da matsalar tattalin arziki da cutar ta haifar a matsayin wata dama ta wadata kansa ta hanyar amfani da damar aka ware wa mabukata.
Staveley mai shekara 54, da abokin aikinsa, David Andrew Butziger mai shekara 53 sun shirya bayanan karya a matsayin masu gidajen abinci guda uku da kasuwancin da ba a aiwatar ba mai suna Dock Wireless duk da suna da manyan albashi kowane wata.
A cewar Ma’aikatar Shari’a Wani dan kasa da ya damu da yanayin yaudararsu ya fallasa su don a yi bincike a kan lamarin.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan wannan lamari na ɗaurawa kai mutuwa da wannan ɗan ƙasar Amurka yayi don jin tabakinku zaku iya biyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci.
KU KARANTA WANNAN:
Manoman Jihar Borno sun fara biyan haraji ga kungiyar ISWAP.
Tofa Wani Matashi Ya Turawa Jarumar Ummi Rahab Wani Zazzafan Sako Domin Ta Share Masa Hawaye
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.