Advertisement
Trending

Tofah Saurayin Daya Tonawa Nuhu Abdullahi Asiri Tare Da Ƙaryata Abunda Ya Faɗa Yanzu Ya Sake Wallafa Wani Batun Game Dashi

Tofah Saurayin Daya Tonawa Nuhu Abdullahi Asiri Yanzu Ya Sake Wallafa Wani Batun Game Dashi

Saurayin Daya Bayyana Asalin Nuhu Abdullahi Jarumin Kannywood, A Yanzu Ya Sake Wallafa Wani Batu Game Dashi.

Kamar Yadda Kuka Sani Bamu Jima Da Kawo Muku Labarin Saurayin Dayayi Dogon Rubutu Akan Rayuwar Nuhu Abdullahi Jarumin Kannywood, Wanda Yake Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Shirin Film Mai Dogon Zango Wato Labarina.

Bayan Hira Da Nuhu Abdullahi, Wanu Saurayi Ya Tona Masa Asiri Yadda Ya Karyata Abunda Ya Fada Acikin Hirar

Sai Dai Bayan Cece-kuce Da Wannan Rubutu Nasa Ya Kawo A Yanzu Ma Ya Sake Wallafa Wani Rubutun Ga Yadda Abun Ya Kasance.

Jiya nayi rubutu akan jarumi NUHU
ABDULLAHI ina kalubalantar sa akan chanza asalinsa dayayi tareda cire sunan mahaifarsa acikin tarihin rayuwarsa Inda wasu suke ganin cewa bankyauta wasuma harda zagina saboda na fadawa duniya gaskiya.

Nikuma sa nake ganin cewa abinda nayidaidai ne dalilina kuwa shine munsan Nuhu Abdullahi tun kafin yazama wani abu
munzauna dashi alokacinda shi bakowabane, dukanin wadanda suke kareshi sun Sanshine bayan daukaka tazo masa.

Alummar garin tudun bichi sune suke sonsa tsakaninsu da Allah domin da adduar suneyazama abinda yazama, sune sukafi kowa yimasa fatar alkhairi ba tareda tsammanin wani abu daga hannunsa ba.

A garin tudun bichi aka haifeshi anan yatashi anan aka fara ginashi ta hanyar bashi ilimin boko dana arabi anan ne yafara koyon rayuwa ingantacciya.

Amma yau anwayi gari Nuhu ne yake kore
kansa daga garin dukda babu wani laifi da akayi masa kowani abu da zaisa ace yatsani
garin.

Kawai saboda kar ayi masa dariya ace
shi dan kauyene, to inaso nayi masa wasu
tambayoyi kamar haka.

1) Meye ribarsa ta jefar da mahaifarsa

2) Meyasa baya alfahari da asalinsa

3) Menene dalilin dayasa yacire sunan jiharsa
da kauyensu acikin rayuwarsa.

Inaso yasani cewa daukaka ba hauka bace
dukkamu munada irin daukakar da Allah yayi
mana, yanzu haka nine shugaban marubutan
kasuwannin jihar lagos kuma nine mataimaki na musamman ga shugaban yan Arewa mazauna jihar lagos wato ALH MUHAMMAD DAN DAMMA YABO Amma duk wandayasanni yasan asalina dom dasunan
kauyemmu nake tutiya.

Wato AYuMutanen kauye sune suke sonka tsakaninsu da Allah kuma sune sukeyi maka fatar alkhairi saboda sun sanka alokacinda bakadakomai.

Mahaifinsa yazauna dakowa lafiya
mutumin kirki wanda baitab kushe asalinsaba duk inda yatafi sai yadawo kauyennan haka kaninsa Allyu haka yayansa abdurahman.

Wannan wani hotone wanda akayi a
makarantar GAISS wasagu a bangon ginin
wasagu house tareda Shehu Saidu Ayu da
Suleiman Tanko dakuma Anas yakubu.

An dauki wannan hoton ne alokacinda nuhuabdullahi yake jss3 ajikin bangon sakaba house ranar talata da yamma kafin ashiga MSS.

Ina kira gareka daka janye kalamanka kanemi gafarar abokanka da yan uwanka akan wofantar dasu dakayi domin sunada hakki akanka kuma sai Allah ya tambayeka.

Dafatar
Allah yabaka ikon gyarawa amen.
Ishaka Usman Wali

Wannan Shien Abunda Ya Wallafa A Shafinsa Na Facebook Akan Nuhu Abdullahi.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Dayakw Faruwa Sannam Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Bayan Mutuwar Mahaifina, Mun Shiga Tashin Hankali Ni Da Mahaifiyata Cewar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din Labarina

Ku Karanta Wannan Labarin:

Bani Da Budurwa Amma Nan Da Wata Biyu Zanyi Aure Cewar Presdo Jarumin Film Din Labarina

Ku Karanta Wannan Labarin:

Me Yasa Mutane Basa Tausayin Baba Dan Audu Ne? Hira Da Rabi’u Rikadawa Kan Cin Zarafin Da Ake Masa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button