Yadda akayi na sami daukaka a shirin fina-finan Kannywood, cewar Azeema Gidan Badamasi

Yadda akayi na sami daukaka a shirin fina-finan Kannywood, cewar Azeema Gidan Badamasi

Jarumar masana’antar kannywood mai tashe a yanzu Hauwa Ayawa wacce aka fi sani da Azima a cikin shirin nan mai dogon zango, Gidan Badamasi, tayi bayani akan yadda ta shahara lokaci guda a masana’antar kannywood.

A wata shira da Daily Trust tayi da ita jarumar ta bayyana cewa, bata taba sanin cewa wata rana zata shahara ba duk ba cewar ta taso tana sha’awar yin fim tun tana yarinya.

Jarumar tayi godiya ga Allah kan wannan matakin daya kaita a masana’antar kannywood, domin a cewar ta bata taba tunanin a cikin dan kankanin lokaci zata ka inda ta kai ba a yanzu.

Sunana Hauwa Ayawa kuma anfi sanina da Azima a masana’antar kannywood, wannan sunan na same shi ne sakamakon taka rawar da nayi a shirin nan mai dogon zango, Gidan badamasi, wanda ake nunawa a tashar Arewa24.

An haife ni a Kaduna nayi makarantar Firamare a nihar Kaduna sannan na tafi makarantar sakandare da mata, GGUSSS kwatarkwashi a jihar Zamfara sannan daga baya na halarci makarantar sanin ilimi na’ura mai kwakwalwa, sai dai ina da niyar naci gaba da karatun jami’a.

Na dade ina sha’awar yin fim domin furodusa ce ta haifeni na taso ina ganin ‘yan fim a gidan mu, an hadani da daya daga cikin Daraktocin masana’antar Muhammad Alfazazi wanda daga bisani ya danya ni a harkar fim a kannywood sannan tun daga wannan lokacin nake taka rawar gani.

Kuma a wajan daukar wani fim ne na hadu da Daraktan fim din, Gidan badamasi, Falalu a dorayi inda ya lura da yadda nake taka rawar gani sannan ya nemi ya sakani a shirin wani fim mai dogon zango, Gidan badamasi, wanda anan na sami suna Azima.

Karanta wannan labarin.

Tirkashi Rundunar ƴansandan jihar Jigawa takama muta biyar 5 bisa Sa hannunsu a kinsan manajan kamfanin three brother dake cikin garin Hadejia.

Karanta wannan labarin.

Bidiyan Yadda Kamfanin Nafeesat Abdullahi Ke Maida Tsohuwa Yarinya, Maida Baka Chocolatee

Karanta wannan labarin.

Tirkashi Ankama wanin mutumin Amurka da laifin Karyar Ya Mutu Don Ya Cinye Bashin Naira Miliyan 223

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button