Jami’ar ilorin ta kori ɗaliban makarantar ta da ya zane malamar su akan taƙi temakamar
Jami'ar ilorin ta kori ɗaliban makarantar ta da ya zane malamar su akan taƙi temakamar.

Jami’ar Ilorin ta kori dabin nan da ya lakada wa malamarsa duka Salaudeen Waliu Aanuoluwa na Sashen nazarin kananan halittu wato Microbiology.
Sanarwar da Darektan Harkokin Makarantar Mista Kunle Akogun ya fitar ta ce an yanke wannan hukuncin ne a gaban Kwamitin Ladabtar da Dalibai wanda Salaudeen ya tsaya gabansa a ranar Litinin.
Kwamitin ya bai wa ɗalibin kwanaki 48 domin ya daukaka kara gaban Kwamitin Shugaban Jami’ar.
Tuni aka mika wa ƴan sanda Salaudeen domin daukar matakin da ya dace a kan shi a cewar sanarwar.
Bayan amsa laifin da ya yi na rashin ɗa’a Shugaban Jami’ar ya ba da umarnin a kori Salaudeen daga wannan jami’a.
Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske ba a kan hujjar da bayar game da dukan malamar da ya yi ko kuma wata hujja da ya bayyana domin kare kansa.
Ana iya tuna cewa Dalatopnews ta ruwaito cewa ɗalibin na aji hudu ya lakada wa wata malamarsa dukan kawo wuka dataƙi ba shi taimakon da ya nema.
Dalibin da aka bayyana inkiyarsa a a matsayin Captain Walz bai yi kwas din da ya wajaba dalibai su yi ba na samun horo da sanin makamar aiki da ake tura dalibai a shekarar gab da ta karshe ta karatunsu ba wato SIWES (Students Industrial Work Experience Scheme).
KU KARANTA WANNAN:
Yadda Nafisat Abdullahi Ta Bayyana Dalilin Rigimarta Da Hadiza Gabon – Wata Sabuwa A Kannywood
Tonon asiri: Yadda Abokiyata tamin tayin Auren mijinta innalillahi ashe….., cewar wata budurwa
An ɗaure wasu mutum biyar da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi shekara 141.
Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.