Masha Allah: Jaruma Mama Daso ta shirya gagarumin biki lokacin data bude wajan ratonta mai suna Daso Event center

Masha Allah: Jaruma Mama Daso ta shirya gagarumin biki lokacin data bude wajan ratonta mai suna Daso Event center

Kamar yadda kuka sani jaruman masana’antar kannywood mata da maza sun bude kamfanoni wanda kasuwancin su zai na kara bunkasa, domin wasu daga cikin su ma ta dalilin hakan jama’a suke mamakin arzikin da Allah ya mallaka musu.

A wannan lokacin ma jaruma Saratu Daso wacce kowa yafi sanin ta da Mama Daso, wanda a yanzu take taka rawar gani a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

Ta shirya shagalin wajan taro nata mai suna Daso “Event center”, wanda aka shirya gagarumin shagali a wajan wanda abokan sana’arta da kuma masoyanta suka halarci wajan domin tayata murna.

Mama Daso ta kasance tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finai hausa ta kannywood, wanda tun kusan farko farkon kafa masana’antar dasu ake damawa sannan kuma sun taka rawar gani sosai.

View this post on Instagram

A post shared by Saratu Gidado Daso (@saratudaso)

Jama’a da dama sunyi tunanin Mama Daso zata daina harkar fim duba da yadda shekarun ta sukayi nisa, sannan kuma yawancin abokananta a yanzu basa harkar fim din.

Amma bisa mamaki a yanzu sai jaruma Mama Daso take nuna kamar yanzu ta shigo harkar fim din duba da yadda tauraruwarta take haskakawa a yanzu, sannan kuma daukakarta take neman tafi ta shekarun baya.

Domin a fina-finan da masana’anyar kannywood take shiryawa a shekarun baya basu sami karbuwa kamar na yanzu ba, domin a yanzu kan jama’a ya waye sannan cigaba ya kara yawaita.

Ko su masu shirya fina-finan sunfi jin dadi harkar a yanzu fiye da shekarun baya domin a yanzu da zarar ka shirya sabon fim zakaga yayi saurin sanuwa a wajan al’umma, domin a kwai cenima da yawa wacce ake harka fina-finai a ciki ba kamar a shekarun baya.

Shi yasa a yanzu zakuga suna samin kudi akai-akai.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuga shagalin da Mama Daso ta shirya na bude gurin taron nata mai suna Daso Event center.

Karanta wannan labarin.

Ina mata masu yada alfasha a dandanlin TikTok ku saurari wannan jawabi domin gujewa shiga hallaka

Karanta wannan labarin.

Budurwar Da ‘Yan Uwanta Suke Zinah Da Ita Ta Dubura Har Ta Haukace, Yanzu Wani Bidiyonta Ya Sake Ɓulla Masha Allah

Karanta wannan labarin.

Bidiyan Yadda Aka Gudanar Da Dinnar Bude Daso Event Center Da Mama Daso Ta Bude Domin Gudanar Da Taro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button