Tirƙashe makarantar da malam Abubakar Gumi yabuɗewa makiyaya dan kawo ƙarshen ta addan cin ƙasarnan ya jawo ce ce kuce a kafar sada zumunta.

Tirƙashe makarantar da malam Abubakar Gumi yabuɗewa makiyaya dan kawo ƙarshen ta addan cin ƙasarnan ya jawo ce ce muce a kafar sada zumunta.

Fitaccen malamin nan na addinin Islama Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya assasa wata makaranta a cikin wani daji domin amfanar makiyaya wajen samun ilimin addini da na zamani.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da Sheikh Gumi ya sha nanata cewa samar da ababen more rayuwa a zamantakewar makiyaya zai taimaka wajen magance munanan akidu na tayar da zaune tsaye.

Gumi ya ce matsalar tsaro a Najeriya musamman ta’adar ƴan fashin daji ka iya zama tarihi muddin an yi musu wani tanadi na samun ilimi da sauran ababen morewa a zamantakewarsu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa makaranar da Sheikh Gumi ya sanya wa suna Cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio tana nan a birtalin kiwo na Kagarko da ke kusa da Kauyen Kohoto a Jihar Kaduna.

Idan aka assasa irin wannan cibiya domin ilimantar da makiyaya a kowa lungu da sako na kasar to kuwa za a samu zaman lafiya a Najeriya.

A maimakon makudan kudaden da gwamnati take kashewa a kan sojoji da kayan yaki ya kamata a rika kashe kudaden domin makarantu da malamai.

Ba sau daya ba tattauna da ƴan daban daji kuma sun bayyana aniyyarsu ta ajiye makamai su rungumi zaman lafiya muddin gwamnati za ta kula da ilimin ƴaƴansu da samar musu sauran ababen more rayuwa a zamantakewarsu.

Abin da ya zaburar da ni na bude wannan cibiyar ilimi shi ne don magance matsalar rashin tsaro da muke fama da ita a kasar nan.

Kasancewar kowane laifi akwai masu aikata shi kuma masu aikata laifuffukan suna da wani dalili wanda kuma wannan dalili muke son ganin mun murkushe.

Mun gano cewa ilimi shi ne zai magance duk wadannan matsaloli na rashin tsaro da muke fuskanta a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa muddin wadanda suke aikata miyagun laifuka a kasar aka yi musu tanadin hanyoyin da za su samu ilimi to babu abin da zai sanya su rika aikata abin da a yanzu ake gani yana faruwa.

Dole ne a tashi tsaye a ilimantar da su wanda hakan ya sanya muka assasa wannan cibiya domin ta zamanto abun koyi ga gwamnati a kowane matakinta da masu hannu da shuni da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Ya kamata a hada kai wajen tunkarar bukatun makiyaya da ke rayuwa a cikin dazuka wanda ba su bukatar sai an kashe wasu makudan kudade kuma hakan zai taimaka gaya wajen samun zaman lafiya.

Yanzu abin da muke da shi a kasa a wannan cibiya tana kunshe da azuzuwa guda shida da za a iya amfani da su a matakin karantarwa na Firamare da Sakandire a kowane lokaci.

Ana iya karantarwa a kowane lokaci domin kuwa makarantar za ta riga gudana ne a tsawon sa’a 24 da ake da ita duk rana saboda yadda makiyaya ke fita kiwo tun daga misalin karfe 10 na safe kuma ba za su dawo ba har sai rana ta fadi.

Saboda haka suna da sa’a biyu zuwa uku da za su iya daukar darasi kafin su fita kiwo, sannan kuma akwai fitilu da za mu sanya masu amfani da hasken rana saboda su samu damar yin bitar karatuttukansu idan dare ya yi.

Idan aka assasa makamanciyar wannan cibiya ko’ina a fadin kasar nan yan Najeriya za su zauna cikin aminci in ji sheak Abubakar Gumi.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan Wannan lamari na shawarar babban malami a sheak Abubakar Gumi.

KU KARANTA WANNAN:

Tofa mayaƙan ISWAP sun sake kai hari garin Askira Uba dake jahar Barno.

Nuhu Abdullahi Ya Ɗauki Mataki Akan Saurayin Dayake So Ya Tona Masa Asiri Tare Da Ƙaryatashi

Tirkashi Rundunar sojojin Nigeriya ta kashe mayaƙan ISWAP mutum 50 a Wani saban harin ramuwar gayya akan kisan janar ɗin sojojin.

A ranar Litinin mutum 12 aka kashe a Illela yayin da kuma ragowar ukun suka rasa rayukansu a Goronyo a jihar Sokoto.

 

Duk Namijin Danaji Muryarsa Sai Sha’awata Ta Tashi Na Zubar Da Maniyyi Cewar Wata Budurwa ‘Yar Shekara Ashirin

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button