Tofa Ango A Hanun Hukuma ,Yan Sanda Sunyi Ram Da Ango Ta Bin Didigin Fostar Aurensa Kan Zargin Fashi Da Makami

Tofa Ango A Hanun Hukuma ,Yan Sanda Sunyi Ram Da Ango Ta Bin Didigin Fostar Aurensa Kan Zargin Fashi Da Makami

Wata Sabuwa Inji Yan Caca Wani Mai Shirin Zama Ango Ya Shiga Hannun Yan Sanda Ana Saura ‘Yan Kwanaki Aurensa

An Bankado Angon Wanda Ake Zargi Da Hannu A Wani Fashi Da Makami Da Ya Wakana Da Taimakon Fostar Aurensa Da Aka Manna A Wurare

A Ranar Laraba Ne Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kama Wani Direban Keke Napek Wanda Ake Shirin Daura Ma Aure A Ranar Asabar, 13 Ga Watan Nuwamba

Pulse Nijeriya Ta Rawaito Cewa An Damke Mai Shirin Zama Ango Ne Bayan Wasu Mutane Da Aka Kama Bisa Laifin Fashi Da Makami Sun Ambace Shi A Matsayin Shugaban Kungiyar Su

Rundunar ‘Yan Sanda Jihar Delta Ta Kama Wanda Ake Zargi Mai Suna Festus Bisa Zarginsa Da Hannu A Wani Fashi Da Makami A Yanki Sapela

Hotunan Auren Wanda Ake Zargin Da Amaryarsa Ne Yayi Ta Yawo Inda Aka Manna Fostar Aure Nasu A Wurare Da Dama, Sannan An Bayyana Cewa Zasu Shiga Daga Daka A Ranar Asabar 13 Ga Watan Nuwamba A Cocin Onghenetega Baptist Church A Sapela

Saide Kuma Bayan Yan Fashi Da Aka Kama Sun Tona Masa Asiri Sai Jami’an Yansanda Suka Bankado Direban Adaidaitan Sannan Suka Kamashi A Unguwarsa

A Cewar Wani Rahoto Daga Shafin Correctng.com Shaidun Sun Ce Festus Ya Ce Bai San Komai Ba Akan Lamarin Lokacin Da Yan Sanda Suka Kamashi Inda Yace Tuggu Aka Shirya Masa

Ya Fara Da Cewa Mutanen Da Basa San Cigabansa Ne Ke Kokarin Shafa Masa Bakin Fenti A Laifin Da Bai San Komai Ba

A Halin Da Ake Ciki , Kamun Festus Yasa Zance Auren Ya Sha Ruwa Sanna Kuma Ya Kunyata Amaryarsa , Wacce Da Yanzu Suna Tare

Ku kalli Bidiyan Anan

Tofa Masu Sauraran Mu A Koda Yaushe Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci.

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

Dauda Kahutu Rarara Ya Bawa Saratu Daso Mamaki A Wajen Taron Bude Gidan Biki Da Tayi

Bidiyan Yadda Aka Gudanar Da Dinnar Bude Daso Event Center Da Mama Daso Ta Bude Domin Gudanar Da Taro

‘Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Shugaban Kamfanin Three Brothers Sun Kasheshi Da Matarsa

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button