Tofa mayaƙan ISWAP sun sake kai hari garin Askira Uba dake jahar Barno.
Tofa mayaƙan ISWAP sun sake kai hari garin Askira Uba dake jahar Barno.

Ana zargin mayakan Kungiyar ISWAP masu da’awar jihadi a Yammacin Afirka sun sake kai hari Karamar Hukumar Askira Uba da ke Jihar Borno.
Wakilinmu na Dalatopnews ya ruwaito mana cewa mayakan sun cinna wa gidaje da dama wuta a kauyen Dille.
Wata majiya ta shaida wa Dalatopnews cewa maharan sun kutsa kauyen ne da misalin karfe 5.30 na yammacin ranar Litinin.
Majiyar ta ce mayakan sun yashi kayayyaki masu tarin yawa a shaguna musamman kayyayakin abinci, sannan daga bisani suka cinna wa gidajen mazauna kauyen wuta.
Sai dai har ya zuwa lokacin kawo wannan rahoto, babu wani karin bayani dangane da girman ta’asar da maharan suka tafka.
Kwanaki biyu da suka gabata ne mayakan ISWAP suka yi wa garin Askira dirar mikiya da misalin karfe bakwai na safiyar Asabar a cikin jerin gwanon motoci, suna luguden wuta babu kakkautawa.
A yayin harin na kwanton baune ne mayakan na ISWAP suka harbe wani Birgediya Janar din sojoji da kuma wasu sojojin hudu a Bulguma wani yanki mai tazarar kilomita kadan da garin Askira na Karamar Hukumar Askira Uba a Borno.
mayakan sun kashe Birgediya Janar Dzarma Zirkusu, wanda tuni Babban Hafsan Sojojin ƙasar na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya jajanta wa iyalansa da sauran sojojin da suka riga mu gidan gaskiya.
Kamar yadda muka kawo muku rahoto jiya Bayanai sun ce sojojin Najeriya sun aika kwamandojin ISWAP 50 lahira a wani harin ramuwar gayya da suka kai wa kungiyar bayan harin da ya yi ajalin Birgediya Janar Dzarma Zirkusu.
KU KARANTA WANNAN:
Tofa In Baba Dan Audu Ne Babanka Wane Mataki Zaka Dauka Akansa ?, A Matsayinka Na Mai Hankali
Kada Kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.