Sama da ɗalibai dubu 80 ke cikin barazanar rasa gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare a jihar Kano.
Sama da ɗalibai dubu 80 ke cikin barazanar rasa gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare a jihar Kano.

Sama da ɗalibai dubu 80 ke cikin barazanar rasa gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare
Wannan yanayi da ɗaliban suka tsinci kansu na da alaƙa da gazawar gwamnatin jihar na biyan kuɗaɗen da hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Najeriya wato NECO ke binta.
Kashi 70 cikin 100 na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar ta shekarar 2021 iyayensu ne suka biya musu kuɗin jarrabawar amma har yanzu babu labarin sakin jarrabawar tasu.
Wannan yanayi da ɗaliban ke ciki ya ja hankali abin da ya kai ga ƙungiyoyin masu fafutika jan hankalin gwamnati don ganin yaran ba su rasa damar ci gaba da karatu a wannan zangon ba.
Jihar Kano na cikin jihohi irin su Adamawa da Neja da Zamfara da NECO ta ce tana bi miliyoyin naira na bashi kuɗin jarrabawar ɗalibansu.
Ɗaya daga cikin ɗaliban da wannan lamari ya shafa ya shaida wa manema labarai cewa suna cikin tasku domin makarantun gaba da sakandare na gab da rufe gurbin ɗaukan ɗalibai a zangon karatun bana.
Ya ce yana dakon jarrabawar ne domin shiga jami’ar da ya nema kuma da alama idan aka ci gaba da fuskantar wannan tsaiko watakila ya rasa damarsa.
Mun yi yunƙurin tuntuɓar makarantarmu amma sai a ce mu sake haƙuri ga shi lokaci na wucewa ban san makomata ba a yanzu.
Wannan yanayi da ake ciki ya tilasta wa wasu masu fafutika aike wa gwamnati wasiƙar da ke bayani kan halin da ɗaliban ke ciki da kuma neman daukan mataki.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari na jihar Kano don jin tabakinku zamuso mukarɓi ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Saboda Isah Ali Pantami Musulmi Ne Akeyi Masa Hassada Cewar Feni Fanni Kayode
Jami’ar ilorin ta kori ɗaliban makarantar ta da ya zane malamar su akan taƙi temakamar
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.