Subhanillahi Yadda Wani Matashi Ya Mutu A Hannun Yan Vigilante Bayan Mahaifinsa Ya Kaishi A Masa Hukunchi
Subhanillahi Yadda Wani Matashi Ya Mutu A Hannun Yan Vigilante Bayan Mahaifinsa Ya Kaishi A Masa Hukunchi

Wani Matashi Mai Suna Haruna Auwal Ya Rasu A Ofishin Yan Vigilante Bayan Da Mahaifinsa Auwal Ado Ya Kaishi Ayi Masa Hukunchi Saboda Ya Kangare
Lamarin Ya Faru Ne A Kauyen Kafin Gana Dake Karamar Hukumar Birinin Kudu Dake Jihar Jigawa
Tun Da Fari Dai Shi Auwal Ana Zargin Dansa Da Satar Masara A Gonar Mutane , Inda Sakamakon Bacin Rai, Sai Ya Kaishi Ofishin Yan Vigilante Da Aka Fi Sani Da Yan Bulala Domin Hukunta Shi
Bayan Ya Kai Marigayin , Sai Yan Bulala Din Suka Hukuntashi Ta Hanyar Bashi Gwale Gwale Inda Daga Nan Ne Sai Jikinsa Ya Rikice Har Aka Karzaya Dashi Asibiti
Bayan An Kaishi Asibiti Ba’a Dade Ba Kuwa Sai Haruna Yace Ga Garin Ku Nan
Kakakin Rundunar Yan sanda Jihar Ta Jigawa Asp Lawan Shisu Adam Ya Tabbatar Da Faruwar A’amarin
Kakakin Ya Kuma Tabbatar Da Cewa Tuni Suka Cafke Mahaifin Marigayin Da Kuma Wani Mutum Daya Sannan Za’a Fadada Bincike
Ya Kuma Kira Ga Iyaye Dasu Rika Yiwa Yayansu Hukunci Mai Sauki Domin Gujewa Nakasa Ko Ma Rasa Rai Baki Daya
Allah Ya Kyauta Wannan Shine A Karin Kyarin Gira An Tabo Ido Ya Kamata De Iyaye A Kiyaye Duka Bawa Kyara Add’a Itace Mafita
Masu Karatu Bayan Kun Karatan Wannan Labarin Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci.
Ku Kara Karanta Wannan Labarin
‘Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Shugaban Kamfanin Three Brothers Sun Kasheshi Da Matarsa
Tofa mayaƙan ISWAP sun sake kai hari garin Askira Uba dake jahar Barno.