Advertisement

Wata Sabuwa Yan Sanda Sun Cafke Saurayi Da Yake Yaudarar Yan Mata Ya Gudu Da Wayarsu Ta Salula

Wata Sabuwa Yan Sanda Sun Cafke Saurayi Da Yake Yaudarar Yan Mata Ya Gudu Da Wayarsu Ta Salula

Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Kano Ta Cafke Wani Saurayi Mai Suna Muhammed ,Wanda Ya Kware Wajen Yaudarar Yan Mata Yace Ya Na Son Su , Inda Daga Budurwa Ta Saba Da Shi ,Sai Ya Yaudaraita Ya Gudar Mata Da Wayarta Ta Salula

A Wata Sanarwa Da Kakakin Rundunar Yan Sanda ,Abdullahi Kiyawa Ya Fitar A Yau Laraba , Dubun Matashin Ta Cika Ne Bayan Da Wata Budurwa Da Ke Zaune A Sharada Ta Kai Karar Muhammad Saifullahi Ofishin Yan Sanda Na Yankinsu Cewa Ya Yaudaraita Ya Gudar Mata Da Wayar Ta

Tace Matashin Yazo Gidansu Ne Ya Kuma Nuna Yana Son Ta Ita Kuma Ta Amince Dashi , Amma Da Ga Bisani Sai Ya Karbe Mata Wayarta Da Ta Kaninta Ya Ari Kafar Zomo

Budurwar Tayiwa Ofishin Karin Bayani Da Cewa Lokacin Da Ya Karbe Musu Wayoyin, Sai Ya Wayance Da Cewa Ya Yar Da Mukullin Babur Dinsa , Inda Bayan Sun Taya Shi Nema, Kuma Suna Tsaka Da Nema Ne Ya Arce Ya Kuma Kashe Wayoyin

Kiyawa Ya Kara Da Cewa Jin Haka ,Sai Kwamishinan Yan Sanda, Sama’ila Shu’aibu Ya Umarchi Dakarun Kan-Ka-Ce-Kwabo , Wato Puff Ada, Karkashin SP Abdulrahim Adamu Da Su Shiga Farautar Matashin

Kwamishinan Ya Kuma Umarchi Kakakin Rundunar Da Ya Kwarmata Neman Matashin A Gidajen Rediyo Da Talabijin

Daga Nan Ne Yan Sanda Suka Shiga Farautar Sa Har Suka Cafke Shi A Titin Gidan Zoo

Inda Matashin Ya Amsa Laifinsa , Inda Kakakin Yace Ana Cigaba Da Bincike Kuma Za’a Gurfanar Dashi A Gaban Kuliya Kamar Yadda Shafin Daily Nijeriya Ta Rawaito

Masu Karatu Bayan Kun Karanta Wanna Labari Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci.

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

Tofa mayaƙan ISWAP sun sake kai hari garin Askira Uba dake jahar Barno.

Bidiyan Yadda Aka Gudanar Da Dinnar Bude Daso Event Center Da Mama Daso Ta Bude Domin Gudanar Da Taro

Ina mata masu yada alfasha a dandanlin TikTok ku saurari wannan jawabi domin gujewa shiga hallaka

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button