Wani sabon cece-kuce ya barke bayan da jama’a suka ga Rahama Sadau a dawo kannywood da wani sabon salo
Wani sabon cece-kuce ya barke bayan da jama'a suka ga Rahama Sadau a dawo kannywood da wani sabon salo

Shin Rahama Sadau ta dawo Kannywood ne wannan tambayar wasu ne daga cikin masu kallon shirin fina-finan Hausa suke yi, tun lokacin da hotunan ta suka bayyana a wajan daukar fim din barkwanci mai suna Gambo da Sanbo da ake dauka a garin Gombe.
Wanda shirin yana dauke da jaruman kannywood irin su Maganji mijin yawa, Rahama Sadau, Rabi’u Daushe da kuma sani Musa Danja.
Ganin ana daukar wannan shirin daga wata Jiha daga cikin Jihoshin Arewacin Nageriya tare da wasu daga cikin jaruman kannywood, hakan yasa wasu mutanen suke ta tambarya ko Rahama Sadau ta dawo masana’antar kannywood domin cigaba da shirin fina-finan.
Kowa yasan abin da ya faru da Rahama Sadau a shekarun baya wanda aka yi ta dambarwa tsakanin jarumar da kuma abokan sana’ar ta, har ma da sauran al’umma masoya Annabi Muhmmad S.A.W biyo bayan shigar da tayi cikin rashin sa’a wani fajiri matsiyaci ya taba martabar Manzon Allah S.A.W a kasan hoton nata.
Wannan al’amarin ya tada muka sosai wanda har takai ga kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa wato Moppan sun bada sanarwar sun dakatar da Rahama Sadau a karo na biyu, duk ta fito tayi kuka sannan ta nemi yafiyar al’ummar Annabi.
Sannan kuma ta bada tabbacin cewa bada masaniyar faruwar hakan tayi wannan hoton ba, amma haka ta dauki wannan laifin tun da itace sanadi ta kuma tuba tayi alkawarin hakan bazata sake faruwa ba.
Sai dai kawo iyanzu babu wata sanarwa a rubuce ko aikace data bayyana janye korar da aka yiwa Rahama Sadau daga masana’antar kannywood ko wani abu mai kama da haka, wanda ita kuma Rahama Sadau ba’a sake ganinta a wani shirin fim ba tun bayan faruwa lamarin.
Hatta shirin da take mai dogon zango na ‘yar Minista wanda take haskawa a tashar ta dake kan manhajar Youtube, ta dakatar da shi a kashi na takwas 8 baci gaba ba.
Wannan kana daga cikin labarin kenan domin kuji cikekken labarin kai ku kalli bidiyon dake kasa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.
Karanta wannan labarin.
Yadda matata ta daure ni a jikin gado tamin shegen duka sannan ta gudu gidan su sabida ta fini karfi
Karanta wannan labarin.
Tirƙashi a daran jiya Laraba motar barasa ta faɗi a gaban ofishin shizba a jihar kano.
Karanta wannan labarin.
Wata Sabuwar Magana Soyayya Ce Wannan Ko Kungiyar Moppan Ta Janye Korar Da Tayiwa Rahma Sadau