Innalilahi waina ilaihir rajiun Allah yayiwa ƴan mata ba kwai 7 rasuwa a hatsarin jirgin ruwa.

Innalilahi waina ilaihir rajiun Allah yayiwa ƴan mata ba kwai 7 rasuwa a hatsarin jirgin ruwa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan mata bakwai sun rasa rayukansu bayan da kwale kwalen da suke tafiya a ciki ya kife ranar Alhamis da dare a Jihar Jigawa.

 lamarin ya faru ne lokacin da suke kokarin tsallaka wani kogi a kan hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi a garin Gasanya.

Bayanai sun ce jirgin na dauke da mutum 12 ne lokacin da ya kife a cikin kogin wanda ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa inda bakwai suka rasu biyar suka tsallake rijiya da baya.

Mutanen dai na kan hanyarsu ne ta komawa garinsu na Gafasa da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa daga Gasanya na Karamar Hukumar Auyo.

Malam Mikail Jibril daya ne daga cikin iyayen waanda suka rasu kuma ya shaida wa manema labaranmu cewa shekarun ƴan matan bai wuce 11 ba zuwa 12.

Mai garin na Gafasa Alhaji Adamu Abdullahi ya ce tuni aka yi jana’izarsu.

A watan Mayun wannan shekarar mutum fiye da 100 sun rasa rayukansu sakamakon irin wannan hatsarin na jirgin ruwa da ya afku kusa da garin Warah na Jihar Kebbi duk a yankin na arewa maso yammacin Najeriya.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku na sakon jajanta wa ga kamar kafin hausa da Auyo baki ɗaya don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye.

KU KARANTA WANNAN:

Yanzu asirin wasu matan Hausawa wanda suke bibiyar Bokaye ya tonu inda ake zina dasu domin bukkatar su ta biya

Tabbas Wannan Waƙar Ta Naziru Sarkin Waƙa Tana Saka ‘Yam Mata Da Samari Shauƙi

Bidiyan Yadda Wasu Amare Suka Fara Bayyana Tsaraichinsu Tun A Pre Weeding Picture

Kimanin mutane 84 ne suka mutu a hatsarin mota wasu kuma suka samu munanan raunuka a Jihar Gombe.

Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button