Innalilahi wainna ilaihir raji’un Allah yayiwa angon dake shirin angon cewa rasuwa 11 December 2021 maisuna sani Ruba.

Innalilahi wainna ilaihir raji'un Allah yayiwa angon dake shirin angon cewa rasuwa 11 December 2021 maisuna sani Ruba.

 Wani matashin da ke shirin angwancewa a ranar 11 ga watan Disamban 2021 Allah yamasa rasuwa.

Kamar yadda mukasani kullunafsin za ikatul maut dukkan mai rai mamacine a safiyar yaune muka sami wani rahoto a kafar sada zumunta rahotan dake nuna saurayin dake shirin angwancewa Allah ya karɓi rayuwarsa.

Yana dai shirin angwancewa ne da fitacciyar ƴar kasuwar kafar sada zumunta ta zamanin nan Rafeeah Zirkarnain.

Masoyiyar mamacin ce ta fara wallafa labarin rasuwarsa a shafinta na Facebook da misalin karfe 7:00 na daren ranar Alhamis wanda take cewa kamar haka.

Innalillahi wa Inna ilaihir raj’iun masoyi Sani Ruba ashe ba za mu kasance mata da mijin ba a ranar 11 ga Disamba Tun jiyan nake jin wani yanayi a raina amman na rike tunanin a raina Ba zan taba samun mutum irinka a matsayin miji ba kamar yadda ta wallafa a shafin nata na Facebook.

Sani mai shekara 36 a duniya dan asalin garin Ruba ne da ke Jihar Jigawa wanda yanzu yake zaune a garin Jos na Jihar Filato.

Rahotanni sun ce matashin angon ya gamu da ajalinsa ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan titin Numan zuwa Gombe a ranar Alhamis.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin amaryar amma hakan ya ci tura saboda ta gaza daukar wayata ko amsa sakon kar ta kwanan da ya tura mata saboda kaduwa da dimuwar da take ciki Faransa koyan.

Kazalika Kafin rasuwarsa marigayin ya yi karatu a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Tuni dai mutane da dama ciki har da malamansa na jami’ar suka shiga nuna alhininsu tare da mika sakon ta’aziyya ga iyaye da abokai da kuma amaryar tasa wadda mutuwa ta yi musu yankan kauna.

To jama’a a harkulum Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews ɗauke da labaran duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Yanzu wani sabon al’amari ya bulla akan naiman taimakon al’umma ga jinyar jarumi Sani Garba SK kannywood

Nigeria Railway Corporation (NRC) za ta yi asarar miliyoyin naira yayin yajin aikin na kwana uku Idan ba a biya musu abinda suke so ba.

Mawakin Kudu Davido Ya Tada Hankulin Mawaka Da Jaruman Kudi Har Da Na Kanywood

Yadda Zaku Gane Matar Auren Datake Zinah Ta Kafarta Cewar Malam Abdullah Gadon Kaya Kalli Sabon Wa’azinsa

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button