Kimanin mutane 84 ne suka mutu a hatsarin mota wasu kuma suka samu munanan raunuka a Jihar Gombe.
Kimanin mutane 84 ne suka mutu a hatsarin mota wasu kuma suka samu munanan raunuka a Jihar Gombe.

Kimanin mutane 84 ne suka mutu a hatsarin mota 350 wasu 939 kuma suka samu munanan raunuka daga watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar 2021 a Jihar Gombe.
Kamar yadda mukasani hatsarin mota yazama wani abu da saidai muce inna lillahi wainna ilaihir wanda a koda yaushe yana faruwa a kowani yankin a faɗin duniya saida wani abu guda ɗaya.
Wannan abun ba komai bane face irin motocin da muke hawa dakuma irin lodin da muke yiwa motocin namu saikuma irin jan da muke yiwa motocin wannan na ɗaya daga cikin abun da suke kawomana hatsarin motar a faɗin kasarmu dama yankin arewa bakiɗaya.
Baya da wannan musami rahoto irin hastarirrikan da suka auku a jihar Gombe dama adadin wanda suka jikka
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Ishaku Gabmi Ibrahim ne ya bayyana hakan a kididddigar rahoton hukumar da ya fitar ranar Alhamis.
A cewarsa haduran sun ritsa da fasinjoji 1,548 ne a cikinsu 525 kuma suka tsira ba su samu rauni ba.
Kwamandan ya ce daga watan Janairu zuwa Maris an samu aukuwar hadura guda 102 inda mutum 32 suka mutu wasu 298 kuma suka ji rauni.
Kazalika ya ce a tsakanin watan Afirilu da Yuni an samu mutuwar mutum 32 wasu 319 suka ji rauni sannan wasu 16 ma suka mutu 269 suka samu raunuka a tsakanin watan Yuli zuwa watan Satumba.
Ishaku ya kuma ce a tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba kuwa an samu mutum hudu da suka mutu 53 suka ji rauni a wasu hadura 22 daban daban da suka faru.
Daga nan sai Kwamandan ya roki direbobi da sauran masu amfani da hanyoyi da su zama jakadun hanya na gari wajen bin dokokinta domin gujewa asarar rayuka ta dalilin faruwar haduran Aban hawa na yau da kullum.
KU KARANTA WANNAN:
Ado Gwanja Yasha Zagi Da Tsinuwa Bayan Ya Turawa Davido Dubu Goma A Kyautar Birthday Dinsa
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.
One Comment