Nigeria Railway Corporation (NRC) za ta yi asarar miliyoyin naira yayin yajin aikin na kwana uku Idan ba a biya musu abinda suke so ba.

Nigeria Railway Corporation (NRC) za ta yi asarar miliyoyin naira yayin yajin aikin na kwana uku Idan ba a biya musu abinda suke so ba.

Ma’aikata sufurin jiragen ƙasa na zanga zangar lumana saboda ƙarin albashi.

Kamar yadda muka sani a kwanakin baya an kawowa mutanan  dake zirga zirga akan jirgin ƙasa hari dama ma aikata baki ɗaya wanda akan hanyarsu tazuwa Abuja ƴan bindiga suka samu su abun fashewa wanda hankalin jama’a yatashi sosai.

Baya da haka a jiyama mun samu rahoton dake nuna na mana cewa ma aikata jirgin ƙasan naso a ƙara musu albashinsu wannan dalilin yasa suka tsiro zanga zanga da kuma shiga yajin aiki akan lamarin.

Dubban ma’aikatan hukumar zirga-zirgar jiragen ƙasa a Najeriya sun tsayar da ayyuka cak a faɗin ƙasar domin matsa wa gwamnati ta ƙara musu albashi da kuma kula da walwalarsu.

Tuni tashoshin jirgin suka kasance a rufe, yayin da wakilinmu na Dalatopnews Abdullahi Usman Ahmad ya tarar da ma’aikatan ɗauke da kwalaye suna zanga-zanga a tashar jirgi ta Idu da ke Abuja wadda ke danganewa da Jihar Kaduna.

Ana sa ran hukumar Nigeria Railway Corporation (NRC) za ta yi asarar miliyoyin naira yayin yajin aikin na kwana uku.

Ma’aikatan sun ce za su fara yajin aikin ne daga safiyar yau Alhamis18 zuwa 21 ga watan Nuwamba a matsayin gargaɗi ga gwamnati.

Sai dai hukumar ta ce yanzu haka tana kan tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikatan domin sasantawa.

To jama’a a harkulum Kuna tare da ni A. Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews ɗauke da labaran duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Mawakin Kudu Davido Ya Tada Hankulin Mawaka Da Jaruman Kudi Har Da Na Kanywood

Yadda Zaku Gane Matar Auren Datake Zinah Ta Kafarta Cewar Malam Abdullah Gadon Kaya Kalli Sabon Wa’azinsa

Dadina Da Dan Adam Mantuwa Yanzu Duk Ciwon Da Kikasha Fama Bai Isheki Nutsuwa Ba Maryam Yahaya

Shugaban ƙasa ya ba wa sojoji umarni su tura karin makamai zuwa Sakkwato.

Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button