Trending

Tirkashi Ashe Waɗanann Jaruman Ne Kawai Suka Taimakawa Sani Garba SK A Rashin Lafiyarsa Da Kudade Duk Masana’antar Kannywood

Tirkashi Waɗanann Jaruman Ne Kawai Suka Taimakawa Sani Garba SK A Rashin Lafiyarsa Da Kudade Duk Masana'antar Kannywood

Kamar Yadda Kuka Fitaccen Jarumin Film Din Hausa Wanda Akafi Sani Da Sani Garba SK, Yana Fama Da Rashin Lafiyar Datake Wahalar Dashi, Wanda Yana Da Kyau Abokan Aikinsa Su Taimaka masa.

Jarumin Wanda Ya Kasance A Bangaren Barkwanchi Yana Fama Da Wasu Munanan Rashin Lafiya Da Labari Ya Riskemu Na Cewa Ciwon Hanta Ciwon Suga Su Suke Damun Wannan Jarumin.

Bayan Wallafa Bidiyoyi Da Ake Na Jarumin Duba Da Yadda Jikinnasa Yake Ci Gaba, Ana Neman Taimako A Wajen Al’ummah, Sai Muka Samu Wani Bayani Daga Shafin Fauziyya D Suleiman Wato Matar Da Take Kungiyar Nan Ta Creative Helping Needy Foundation (CHNF) Wato Kungiyar Taimakawa Gajiyayyu Da Marayu, Ta Wallafa Jaruman Da Suka Taimakawa Sani Garba SK A Wannan Rashin Lafiyartasa.

fauziyya_d_sulaiman Tace WASU DAGA YAN FIM SUNTAIMAKAWA SANI SK
Mutane suna ta turo min wannan video na Sani Skakan mu taimaka masa, to magana ta gaskiya akwanakin baya ma mun yi posting Sani Sk kuma wasu daga cikin yan fim sun taimaka masa kuma suna kan ci gaba da taimaka masa da al’umar gari, sai dai cutar shi mai cin kudi ce wato ciwon sugar daciwon hanta.

Yanzu haka abdulamart mai_kwashewa ya Bashi Dubu Dari biyar, don a kai shi asibiti, adizatou Wato Hadiza Gabon ta bashi Dubu Dari Biyu da Hamsin,realalinuhu Wato Jarumi Ali Nuhu ya bashi Dubu Dari,aeeshatsamiya_backup ta bayar da Dubu Dari da wasu da yawa da suka bayar daga masana’antar Kannywood din, muna adduar Allah ya saka musu da alkairi.

Kamar yadda muke fada ciwon Sani Sk ciwo ne mai cin kudi, Yan fim suna iyakacin kokarinsu, ammakuma al’umma dan’uwanku ne musulmi Wandawannan yan’uwantakar ta fi ta sanaa za ku iyataimakawa ba tare da cin mutunci kowa ba.

Allah ya ba shi lafiya.

Ku Kalli Wannan Bidiyon:

Zamu So Ku Watsa Wannan Labarin Domin Yaje Kunnen Mutane Dazasu iya Kara Taimakawa Wannan Bawan Allah Din Domin A Samu Wadannan Rashin Lafiyar Tasa Tayi Sauki, Sannan Zamu So Mu Karbi Addu’oinku Na Nema Masa Lafiya Wajen Allah, Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Yanzu wani sabon al’amari ya bulla akan naiman taimakon al’umma ga jinyar jarumi Sani Garba SK kannywood

Ku Karanta Wannan Labarin:

Ado Gwanja Yasha Zagi Da Tsinuwa Bayan Ya Turawa Davido Dubu Goma A Kyautar Birthday Dinsa

Ku Karanta Wannan Labarin:

San zuciya yasa jarumin kannywood Garzaki Miko ya aikata irin abin da mawaki Davido yayi ga masoyan sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button