Yanzu wani sabon al’amari ya bulla akan naiman taimakon al’umma ga jinyar jarumi Sani Garba SK kannywood

Yanzu wani sabon al'amari ya bulla akan naiman taimakon al'umma ga jinyar jarumi Sani Garba SK kannywood

Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya labarin jarumin kannywood Sani Garba SK yayi ta yawo a kafafan sada zumunta, inda yake naiman taimakon al’ummar Musulmai akan jinyar dake damun sa.

To a yau ma mun sake cin karo da wani saban labarin na jarumi Sani Garba SK wanda wata shahararriyar marubuciya kuma shugabar kungiyar nemawa gajiyayyu da marasa galihu taimako, wato Fauziyya D Sulaiman.

Inda take bayyana cewa, wasu daga cikin jaruman masana’antar kannywood sun bada taimakon su ga jarumi Sani Garba SK.

Ga yadda cikekken rahoton yake.

Mutane suna ta turo min wannan video na Sani Sk akan mu taimaka masa, to magana ta gaskiya a kwanakin baya ma mun yi posting Sani Sk kuma wasu daga cikin yan fim sun taimaka masa kuma suna kan ci gaba da taimala masa da al’umar gari, sai dai cutar shi mai cin kudi ce wato ciwon sugar da ciwon hanta.

Yanzu haka @abdulamart_mai_kwashewa ya Bashi Dubu Dari biyar, ya sa kuma an kai shi asibiti, Hadiza Gabon ta bashi Dubu Dari Biyu da Hamsin, Ali Nuhu ya bashi Dubu Dari, Aisha Tsamiya Dubu Dari, da wasu da yawa da suka bayar daga masana’antar Kannywood din, muna adduar Allah ya saka musu da alkairi.

Kamar yadda muke fada ciwon Sani Sk ciwo ne mai cin kudi, Yan fim suna iyakacin kokarinsu, amma kuma al’umma dan’uwanku ne musulmi Wanda wannan yan’uwantakar ta fi ta sanaa za ku iya taimakawa ba tare da cin mutunci kowa ba. Allah ya ba shi lafiya.

Karanta wannan labarin.

Mawakin Kudu Davido Ya Tada Hankulin Mawaka Da Jaruman Kudi Har Da Na Kanywood

Karanta wannan labarin.

Yadda Zaku Gane Matar Auren Datake Zinah Ta Kafarta Cewar Malam Abdullah Gadon Kaya Kalli Sabon Wa’azinsa

Karanta wannan labarin.

Dadina Da Dan Adam Mantuwa Yanzu Duk Ciwon Da Kikasha Fama Bai Isheki Nutsuwa Ba Maryam Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button