Trending

An Buƙaci Na Zama ‘Yar Maɗigo (Lesbian) A Wani Film Din Kudanchi Cewar Rahama Sadau

An Buƙaci Na Zama 'Yar Maɗigo A Wani Film Din Kudanchi Cewar Rahama Sadau

Shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood, Rahama Sadau, wacce aka kora daga masana’antar Kannywood a kwanakin baya, sananniya ce a gun yan kallo duba da irin tashen da tayi cikin kankanin lokaci daga zuwan ta masana’antar.

Jarumar Ta gamu da tsautsayin da ya fada mataa masana’antar har ya jawo mata kora. tarihi dai ya nuna itace jarumar film ta farko da aka Taba korarta a masandantar.

A wata hira da tayi da kafar yada labarai ta THE GUARDIAN, tauraruwa Rahama ta bayyana cewa an so tafito a wani fim din ta na kudu a matsayin yar
madigo wato lesbian, amma sai ta ki yadda saboda la’akari da daga inda ta
fito Wato arewachin Nigeria.

da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damanmaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin Duniya.

Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin
bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da
hakan.

Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba
dai dai bane ba a rika yi mata kallon ‘yar iska don kawai tana
Sand ar ta.

Ga Bidiyon Sai Ku Kalla Kuji Cikakken Bayani:

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Game Da Abunda Rahama Sadau Tace, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Dole Mutane Dayawa Suna Ganin Bala’i Da Masifa A Rayuwarsu Kalli Tarihin Rayuwar Budurwar nan innalillahi

Ku Karanta Wannan Labarin:

Subhanillahi Yadda Dalibar Jami’ar Umaru Yar Adu’a Dake Katsina Tasha Guba Kan Sabani Da Suka Samu Da Saurayinta

Ku Karanta Wannan Labarin:

Dadina Da Dan Adam Mantuwa Yanzu Duk Ciwon Da Kikasha Fama Bai Isheki Nutsuwa Ba Maryam Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button