Hara haran ƴan bindigar jihar neja yasa an hana hawa wasu samfarin mashin mai ƙafa biyu a faɗin jihar baki ɗaya.
Hara haran ƴan bindigar jihar neja yasa an hana hawa wasu samfarin mashin mai ƙafa biyu a faɗin jihar.

Hara haran ƴan bindigar jihar neja yasa an hana hawa wasu samfarin mashin mai ƙafa biyu a faɗin jihar.
Bayan matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar da kuma karuwar bukatar baburan da ƴan bindiga ke yi madadin karbar kudin fansar wadanda suka yi garkuwa da su.
Sanarwar da Ahmad Ibrahim Matane ya fitar ta ce daga cikin baburan da aka haramta sayarwa akwai Bajaj Boxer Qiujeng Honda ACE Jingchen da sauran babura wanda karfin injinsu ya kai 185cc zuwa sama.
Matane ya ce gwamnatin ta kirkiro wannan mataki ne a kokarin da take ci gaba da yi na hana ƴan bindiga sakat da sauran masu tayar da zaune tsaye a jihar.
Sakataren ya ce gwamnati tana Allah-wadai da irin kashe-kashen da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke yi a wasu sassan jihar lamarin da ta jaddada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta ga bayansu.
Kazalika Matane ya ce gwamnati bazata manta da halin da wadannan matakai za su jefa al’ummar jihar ba sai dai ya ce an dauke su ne da manufar tsare rayuka da dukiyoyin al’umma inda ya yi kira ga dillalan babura a fadin jihar da su bai wa gwamnatin hadin kai.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su bai wa gwamnati da sauran hukumomin tsaro hadin kai a yayin da babu dare babu rana suke fadi-tashin ganin an kawo karshen ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar.
Sakataren Gwamnatin ya kuma umarci hukumomin tsaro da ke jihar da su tabbatar an kiyaye wannan sabbin matakai da aka shimfida.
Matane ya kuma sake nanata cewa haramcin da aka sanya wa ayyukan ƴan Kabu-Kabu da masu Acaba wanda aka fi sani da Okada na nan daram a birnin Minna da kewaye.
Ana iya tuna cewa gwamnatin Jihar Neja ta sanya dokar da ta takaita zirga zirgar babura masu kafa biyu daga karfe 6 na yamma zuwa na safe.
KU KARANTA WANNAN:
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.
One Comment