An kashe mutum 13 ciki har da yara uku wasu mutane 20 kuma sun ɓata ba a san halin da suke cikiba.

An kashe mutum 13 ciki har da yara uku wasu mutane 20 kuma sun ɓata ba a san halin da suke cikiba.

Mazauna yankin Manga wani gari da ke kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru wanda ƴan tawayen kasar na Ambazoniya suka kai wa hari a makon da ya gabata

A yammacin yaune muka sami wani saban rahoto daga yankin bodar Kamaru zuwa Nigeria wanda rahoton ke cewa wani ƙaramin ƙauye dake ƙarshen bodar Nigeria wasu yan tawayen ambazoniya sun

Kakakin al’ummar yankin Abubakar Manga ne ya shaida wa wani kwamiti da gwamnatin Jihar ta kafa kan lamarin lokacin da kwamitin ya ziyarcesu ranar Asabar.

Ya ce in ban da taimakon wani jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da ya kai musu dauki da sai ƴan tawayen sun ga bayan ilahirin yankin.

Malam Abubakar ya kuma shaida wa kwamitin cewa ƴan tawayen kasar Kamarun na Ambazoniya sun tsallaka wani rafi ne sannan suka mamaye yankin nasu ta kan wasu tsaunuka da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce da farko sun fara kai hari ne gidan Dagacin garin inda suka kashe shi kafin daga bisani su shiga harbin kan mai uwa ja wabi har suka kashe mutum 13, ciki har da kananan yara guda uku.

Sun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta girke musu jami’an tsaro a yankunan kan iyakokin domin tabbatar da tsaron ƙasar

Shi ma da yake nasa jawabin Shugaban Karamar Hukumar Takum Mista Tikari gargadin ƴan tawayen ya yi kan tsallakowa su kawo hari Najeriya inda ya ce ba za su lamunci hakan ba a nan gaba.

Shi kuwa Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Danjuma Adamu ya bayar da tabbacin girka jami’an tsaro ya yi a yankin tare da kiran sojoji da su kafa sansaninsu a dukkan yankunan kan iyaka, kamar yadda yake a baya.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.

KU KARANTA WANNAN:

Ashe wannan dalilin ne yasa jama’a suke cece-kuce da maganganu masara dadi akan jarumi Lawan Ahmad da Garzali Miko

Wannan Babban Darasine Ga Wayanda Basu San Makiryicin Yan Damfara Da Artificial Karuwai Ba

Bayan mutane sun turawa mawaki Davido kudin daya roka ya aikata wani abu da shi wanda kowa yayi mamaki

Saurayina Yace Bashida Lafiya, Naje Dubashi Yayi Zinah Dani Na Samu Ciki Cewar Wata Budurwa

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button