kashi 25 na mutanen da ke zama a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na amfani da bayan gida wajen biyan bukatun su
kashi 25 na mutanen da ke zama a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na amfani da bayan gida wajen biyan bukatun su

UNICEF ta bayyana Najeriya a matsayin kasar da aka fi samun yawan mutanen da ke bahaya a bainar jama’a wadanda adadin su ya kai miliyan 46.
To jama’a kamar yada a kwanakin baya muka kawo muku rahotan hukumar UNICEF take gudanar da aikin kula da tsaftar muhalli a jihar Jigawa ƙarƙashin jagoranci Alhaji lamari engineer.
Wanda ga rahotan da hukumar tafiyar bayan kamala wasu wuraren da akayi a faɗin ƙasar Nigeria.
Jami’in hukumar Sam Adejo Okedi ya ce duk da ci gaban da aka samu ƴan Najeriya miliyan 46 ke bahaya a fili matakin da ke barazana ga lafiyar jama’a a sassan kasar.
Alkaluman UNICEF da aka gabatar na kananan hukumomin Najeriya 774 sun nuna cewar a kananan hukumomi 10 ne kacal ba a samun masu bahaya a fili, wanda shi ne kashi 10 bisa 100 a Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar an yi nasarar magance matsalar da ake samu na yawaitar masu bahaya a bainar jama’ar a Jihohin Jigawa da Katsina da kuma Binuwe.
Shugaban hukumar UNICEF da ke kula da shiyar Kano da Sakkwato, Maulid Warfa ya bayyana haka inda ya danganta ci gaban da matakin da hukumomin yankunan ke dauka na magance matsalar.
Sashen Hausa na Rediyon Faransa ya ruwaito Warfa yana cewa an samu nasarar dakile wannan dabi’ar ce a kananan hukumomi 21 da ke Katsina da 18 a Jigawa da kuma guda 9 a Binuwe.
Jami’in ya ce kashi 25 na mutanen da ke zama a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na amfani da bayan gida wajen biyan bukatun su na yau da kullum yayin da kashi 35 kuma ke samun kula ta fannin tsafta.
KU KARANTA WANNAN:
Yanzu Bidiyon Gaskiya Ta Bayyana Game Da Mutuwar Jarumin Kannywood Sani Garba SK innalillahi
Allahu Akbar Khulu Nafsin Za’ikhatul Mau Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Jarumin Kannywood Sani Sk
An kashe mutum 13 ciki har da yara uku wasu mutane 20 kuma sun ɓata ba a san halin da suke cikiba.
Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.
One Comment