An kashe wani malami da dalibi a Kwalejin Horas da Ayyukan Kula da Lafiya.
An kashe wani malami da dalibi a Kwalejin Horas da Ayyukan Kula da Lafiya.

An kashe wani malami da dalibi a Kwalejin Horas da Ayyukan Kula da Lafiya.
Tofa a yammacin jiyane muka sami wani saban rahoto daga jihar Legos Wanda rahotan ke nuna mana yadda aka yiwa wani malami kwalleji kinsan Allah wadai.
malamin mai suna Ahmed Saheed a kusa da garin Poka yayin da shi kuma da kuma dalibin mai suna Razak Bakare aka kashe shi a harabar makarantar wanda duk suke yankin Karamar Hukumar Epe a Jihar Legas.
Wata majiya ta ƴan sanda da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce duka kisan guda biyu an yi su ne a lokuta daban daban amma tsirarsu ba ta wuce sa’o’i 48 ba.
Majiyar ta ce dalibin wanda bincike ya nuna an rika fakonsa shi aka fara kashewa a ranar Laraba sannan aka kashe malamin a ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce a halin yanzu dai ana cikin zaman ɗari ɗar a gaba daya yankin na Poka da kwalejin take sakamakon yanayin da mutane suka tsinci kawunansu saboda aukuwar lamuran.
Oba Babatunde Ogunlaja wani basarake a yankin da yake bayyana takaicinsa ya ce wannan al’amari ya ruguza zaman lafiya da kwanciyar hankali da suka saba da shi a garin Noforija
A kan haka ne ya yi kira ga mahukuntan kwalejin da su dasa na’urori masu daukar hoton bidiyo na CCTV camera a ciki da kewayen makarantar.
Ogunlaja ya kuma nemi Gwamna Babajide Sanwo Olu da Kwamishinan ƴan sandan Jihar Legas Hakeem Odumosu da jibge karin jamian tsaro a yankin.
Kazalika ya nemi Gwamnatin Jihar Legas ta sake gina katangar kwalejin da ta dauki tsawon lokaci da faduwa.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Yanzu Bidiyon Gaskiya Ta Bayyana Game Da Mutuwar Jarumin Kannywood Sani Garba SK innalillahi
Allahu Akbar Khulu Nafsin Za’ikhatul Mau Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Jarumin Kannywood Sani Sk
An kashe mutum 13 ciki har da yara uku wasu mutane 20 kuma sun ɓata ba a san halin da suke cikiba.
Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.