Trending

Anaso A Lalatamin Rayuwa Ta Hanyar Yaudarar Mutane Da Sunana Da Kuma Hoto na Cewar Jaruma ummi Shehu

Anaso A Lalatamin Rayuwa Ta Hanyar Yaudarar Mutane Da Sunana Cewar Jaruma ummi Shehu

Jarumar Kannywood Ummi Shehu Wanda Take Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Fina-finan Hausa Ta Gargadi Mutanen Dasuke Amfani Da Sunanta Wajen Yaudarar Mutane A Kafafen Sada Zumunta.

Fitacciyar Jarumar Film Din Hausa Wato Ummi Shehu wanda Take Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Wani Shirin Film Mai Dogon Zango Gidan Badamasi, Ta Karyata Mutanen Dasuke Amfani Da Sunanta Wajen Zaluntar Mutane.

Acikin Wani Bidiyo Da Jarumar Ta Wallafa A Shafinta Mai Tsawon Minti Uku, Jarumar Tayi Cikakken Bayani Akan Cewa Batayin Facebook, Kuma Duk Wanda Yaga Wani Shafi Ko Account Banata Bane, Domin Kuwa Tana Samun Korafi Daga Wajen Mutane Akan Cewa Tana Yaudarar Mutane Akan Kasuwanchinta A Facebook.

Duk Da Dai Wannan Abun Ba Yanzu Aka Saba yinsa Ba, Domin Ya Taba Faruwa Ga Jarumai Da Dama Acikin Masana’antar Kannywood Musamman Mata, Kamar su Aisha Aliyu Tsamiya Da Sauransu, Wadanda Sukeyin Kasuwanchi.

Mutane Suna Iya Budewa Shafi A Facobook Ko Instagram Suna Wallafa Hotunan Kayayyaki Na Kasuwanchi Da Nufin Cewa Jarumar Ce Take Siyar Da Wannan Kaya, Sai Mutum Ya Tura Kudi Yana jiran Kaya Sai Kuma Yaji Shiru.

Baya Da Haka Jaruma Ummi Shehu Ta Gargadi Mabiyanta Da Batayin Facebook, Kawai Abunda Takeyi A Shafukan Sada Zumunta Shine Instagram Da TikTok.

Wadannam Sune Kawai Abubuwan Datakeyi Domin Ta Gudanar Da Harkar Kasuwanchinta, Duk Wani Shafi Da Mutum Yagani Idan Ba Wannan Ba Kada Ya Yarda Dashi.

Wannan Shine Shafinta Na Instagram Mai Mabiya Miliyan Daya Da Dubu Dari Biyu.

Shafin Tiktok Na Ummah Shehu

Wannan Shine Shafinta Na TikTok, Domin Gudanar Da Abubuwanta Har Da Sana’ointa Ga Bidiyon Da Jarumar Tayi Cikakken Bayani Akan Haka.

Zamu so Mu Watsa Bidiyon nan Domin Yaje Kunnen Mutane Dayawa Da Suke Zaton Jarumar Tana Facebook, Ko Kuma Suke Harkar Kasuwanchi Da Masu Amfani Da Sunanta A Shafin Facebook, Saboda Ya Zamto Dakile Wata Barnar.

Sannan Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari, Kada Ku Manta Ku Danna Mana Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button