Trending

An Kama Saurayin Daya Damfari Mata Da Maza 37 A Facebook Da Whatsapp Ta Hanyar Kasuwanchi

An Kama Saurayin Dayake Yaudarar Mutane A Facebook Da Whatsapp Da Sunan Mata

Hukumar Yan sanda sun kama mutumin da ya
damfari mutane 37 ta facebook da WhatsApp a Kano.

Rundunar Yan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta cafkewani fitinannen dan damfara, wanda ya damfarimutane da dama ta kafar sadarwa.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP AbdullahiKiyawa ya fitar a jiya Litinin, mutumin mai suna Aliyu Hussaini dan unguwar Hotoro mai shekara 25, ya kware wajen sanya hotunan atamfofi, shaddoji,
lesuna da sauransu ta kafar facebook ko WhatsApp.

Kiyawa ya ce idan ya saka hotunan, sai mutane su rika nuna bukatar su, sai su daidaita da shi, su aikomasa da kudin kayan amma kuma sai ya yi kememe ya ki aika musu da kayan.

Kakakin ya kara da cewa dubun dan damfarar ta cikane bayan da wata mata daga Yelwa Shandam ta Jihar Filato ta kawo kararsa shalkwatar y’an sandan ta
Kano, inda ta yi korafin cewa wani mutum a facebook mai suna Aliyu Hussaini Salisu ya sanya hotunan lesuna da shaddoji ita kuma ta zabi kala 14 daga ciki.

Matar ta kara da cewa kudin kayan da ta zaba ya kama naira dubu 100, inda ya ce ta aiko masa ta tashar mota ta unguwa uku, shima kuma zai aika mata da kayan ta nan.

Bayan ta aiko masa da naira dari cif-cif, mai makon Hussaini ya aika mata da kayan da ta zaba, kawai sai ya nade tsimmokara har da tsohon gidan sauro a
cikin leda, ya manne da salatif ya aika mata.

Kiyawa ya kara da cewa, da jin wannan korafi na matar, sai Kwamishinan Yan Sanda, Samaila Shu’aibu, Dikko ya umarci dakarun binciken sirri, karkashin
jagorancin DSP Muntari Jibrin Dawanau domin cafkomai laifin.

Ai kuwa ba da dadewa ba, sai wadannan dakaru su kasamu nasarar damke dan damfarar nan a tashar motata unguwa uku, inda a ka samu na’urar laftof da wayaa tare da shi.

Kiyawa ya baiyana cewa, a yayin titsiye da aka yimasa, Hussaini ya amsa laifinsa inda ya ce idan ya karbe kudaden mutane, sai ya toshe su ta facebook
da WhatsApp din.

Kiyawa ya kara da cewa bayan an kama mai laifin, sai ga mutane har 37 sun yi tururuwa sun kawo korafe-korafe a kan sa da cewa ya damfare su har sama da naira miliyan daya.

Kakakin ya baiyana cewa a jiya Litinin a ka kai mai kaifin babbar kotun majistire da ke Ungoggo domin ya girbe abin da ya shuka.

Toh Allah Ya Kyauta Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari.

Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button