Advertisement

Duk Masana’antar Kannywood bani da Uban Gida idan akwai wanda yake ganin shi ne ya fito yayi magana, cewar jarumi Sulaiman Bosho

Duk Masana'antar Kannywood bani da Uban Gida idan akwai wanda yake ganin shi ne ya fito yayi magana, cewar jarumi Sulaiman Bosho

Ficaccan Jarumin Masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood Sulaiman Yahaya Hamma wanda aka fi sanin sa da Sulaiman Bosho, ya bayyana cewa duk da cikar da masana’antar kannywood tayi bashi da wani Uban Gida wanda zai ce shi ya koya masa harkar fim.

Jarumi Bosho ya bayyana hakan ne a lokacin da shira da gidan Jaridar Damukaradiyya, inda jarumin yake bayyana cewa.

Ni harkar fim din nan da ni aka fara ta ina cikin masana’antar kannywood tsawon shekara 30, don haka bani da wani Uban Gida a cikin masana’antar.

Bayan haka ta kara da cewa: Idan kuma akwai wanda take ganin shi ya koya mini harkar fim sai ya fito ya fada.

Sannan kuma ya kara da cewa: Ni dai nasan bani da wani Uban Gida a masana’antar shirya fina-finai ta kannywood, domin ina cikin ta tun farkon kafuwar ta har kawo yanzu.

Game da burin sa da yake bukata ya cika a masana’antar, jarumin ya bayyana cewa.

A gaskiya buri na shi ne mu yi amfani da fim wajen isar da kyawawan dabi’u na Musluci da Kuma al’adun mu a duniya, don haka ina alfahari da harkar saboda sana’a ta ce wadda ta rufa mini asirin.

Don mun samu arziki a cikin ta na yi aure na yi motoci Kuma da ita mu ke ciyar da iyalan mu har ma mu ke yi wa mutane alheri da abun arzikin da mu ke samu, acewar jarumi Sulaiman Bosho.

Karanta wannan labarin.

Tirƙashi a wani sumame da rundunar ƴansandan jihar Jigawa sukayi sun sami nasarar kama masu laifi guda Goma sha bakwai 17.

Karanta wannan labarin.

Tirƙashi Ankama wani magidanci zai saida ƴaƴansa mata biyu a Jihar Akwa Ibom.

Karanta wannan labarin.

Maza ne suke yaudarar mu shi yasa mu ‘yam fim jama’a suke ganin bama son yin aure da wuri, cewar jaruma Zuwaira Abdussalam

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button