Ficaccan jarumin kannywood Ali Nuhu tare da jaruma Aisha Humaira sun wallafa wata bidiyon a Kasar London lokacin da sukaje shakatawa
Ficaccan jarumin kannywood Ali Nuhu tare da jaruma Aisha Humaira sun wallafa wata bidiyon a Kasar London lokacin da sukaje shakatawa

Kamar yadda kuka sani da yawa daga cikin jaruman masana’antar kannywood suna tafiya yawon shakatawa kasar waje da kuma bude ido.
To a wannan lokacin munga Ficaccan jarumin Masana’antar Kannywood Ali Nuhu tate da wata jaruma mai suna Aisha Humaira, sun ziyarci Kasar London domin shakatawa.
Munga yadda jarumar ta wallafa bidiyon a shafinta na sada zumunta Instagram tare da abokin sana’arta jarum Ali Nuhu, inda suke shakatawa tare da jin dadi a Kasar London
Tun a shekaran jiya ne labari tafiyar tasu ya fara yawo a kafafa sada zumunta, inda jarumi Ali Nuhu ya halarci wajan da ake kallon wasan kwallon kafa na “Arsenal da Newcastle.
Ga hotuna da bidiyon jarumi Ali Nuhu tare da abokiyar sana’ar sa Aisha Humaira wanda suka dauka a Kasar London, lokacin da suke je yawan shakatawa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.