Advertisement

Tirƙashi a wani sumame da rundunar ƴansandan jihar Jigawa sukayi sun sami nasarar kama masu laifi guda Goma sha bakwai 17.

Tirƙashi a wani sumame da rundunar ƴansandan jihar Jigawa sukayi sun sami nasarar kama masu laifi guda Goma sha bakwai 17.

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta kama masu laifi guda 17 a wani sumame da ƴansanda suka kai a kananan hukumomin Dutse da Gumel da kuma Ringim.

Kakakin rundunar yansanda ta jiha ASP Lawan Shiisu Adam shine ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse wanda ɗaya daga cikin manema labaranmu na Dalatopnews tasamu.

Inda yace an kai sumamen ne a tsakanin ranakun 17 zuwa 22 ga wannan watan a wannan ƙananan hukumomi na jihar Jigawa wanda cikin ikon Allah ansami nasarar Kamaru.

Yace an kai sumamen ne domin yaki da masu aikata laifuka a fadin jiharnan
Shlisu Adam ya kara da cewa a lokacin sumamen yansanda sun kwace kayayyakin shaye shaye da suka hadar da sholisho da tabar wiwi da kodin da kuma maganin tari na ruwa.

Rahotanni na cewar a ranakun 4 zuwa 10 ga watan da muke ciki ƴansanda sun kama masu laifi 10 a kananan hukumomin Taura da kuma Kiyawa na jiharnan.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari na jihar Jigawa don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye.

A harkulum Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

Tirƙashi Ankama wani magidanci zai saida ƴaƴansa mata biyu a Jihar Akwa Ibom.

Maza ne suke yaudarar mu shi yasa mu ‘yam fim jama’a suke ganin bama son yin aure da wuri, cewar jaruma Zuwaira Abdussalam

Subhanillahi Ya Kamata A Rufe Hanyar Kaduna Saboda Wasu Dalilai Kan Danyen Aikin Da Ake Aikata

 

Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button