Trending

Yanzu Asirin Aljan Ya Tonu Ƙasurgumin Ɓarawon Keke Napep A Jihar Kano

Yanzu Asirin Aljan Ya Tonu Ƙasurgumin Ɓarawon Keke Napep A Jihar Kano

An kama Aljan, kasurgumin barawonbabur mai kafa uku a Kano.

Rundunar Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafkekasurgumin barawon babur mai kafa uku, wanda a kafi sani da adaidaita-sahu a Kano, ko kuma nafe asauran jihohi.

Shi dai wannan barawo mai suna Sabitu Ibrahim,wanda aka fi sani da Aljan, dan kimanin shekaru 18, daga garin Kaburma Yan Daddawa, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano ya ke.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, AbdullahiHaruna Kiyawa ya fitar a jiya Asabar da daddare,gungun yan sanda na sashin Kan-ka-ce-kwabo wanda rundunar ta ke kira da Operation Puff Ada,karkashin jagorancin SP Buba Yusuf ne su ka samu
nasarar kama Aljan.

Kiyawa ya ce an kama shi ne da wani babu mai kafa uku, wanda ya ke dauke da lamba GRR77QA da kumalambar KAROTA KMC 1106.

Kakakin ya baiyana cewa sunan Aljan na cikin jerin sunayen ma su laifi da rundunar ke nema ruwa a jalloKiyawa, mai mukamin DSP, ya kara baiyana cewa ayayin binciken kwakwaf, Aljan ya amsa cewa tabbas ya hada baki da wani su ka tare wani matukin babur mai kafa uku a Dorayi.

Ya kara da cewa Aljan ya bada bayanin cewa bayan sun tare matukin babur mai kafa ukun, sai su ka yi amfani da waya su ka shake wuyanshi da niyyarsu hallaka shi, amma Alah Ya taimake shi va kufce hallaka shi, amma Allah Ya taimake shi ya kufce ya gudu da raunuka a jikinsa.

Bayan nan ne, in ji Kiyawa, sai Alhaj da abokinsa su ka tsere da wannan babur din, inda ya kara da cewa dashine babur din da a ka kama shi da shi.

Da a ka fadada bincike na siri, inji Kiyawa, sai a ka kamo wani Abdullahi Sulaiman mai shekaru 28, danunguwar Gwale da kuma Abubakar Muhammed mai
shekaru 21 dan unguwar Hausawa duk a birnin Kano, bisa zarginsu da siyan wasu sassa na babur din da Aljan ya k5wace, da kuma wani babur mai lamba
FGE212QX, sai kuma lambar KAROTA 4636 KMC, daaka same su a tare dasu.

Kiyawa ya bada lambar waya 08105359575 gawadanda aka sace musu wadannan babura da sutuntubi rundunar, ko kuma su tuntubi kakakin kaitsaye.

Kwamishinan Yan Sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya godewa al’ummar jihar Kano baki daya bisa gudummawa ta addu’a, kwarin gwiwa da kuma goyon baya da suke basu, ya bukaci a cigaba da basu hadin
kai wajen gudanar da ayyukansu.

Toh Allah Ya Kyauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button