Tsawon Shekaru Biyu Mahaifina Da Kakana Sunayin Lalata Dani Cewar Yarinyar ‘Yar Shekara 13
Tsawon Shekaru Biyu Mahaifina Da Kakana Sunayin Lalata Dani Cewar Yarinyar 'Yar Shekara 13

Tsawon Shekaru Biyu Mahaifina Da Kakana
Suna Yi Min Fyade, Cewar Yarinya Mai
Shekaru 13.
Rahotanni daga jihar Osun sun bayyana
cewar, hukumar NSCDC ta jihar ta kama
mahaifi da kakan wata yarinya mai shekaru 13 da suka yi mata fyade.
Mai magana da yawun shugaban hukumar
Mr Adigun Daniel ne ya sanar da hakan a
ranar Litinin ga manema labarai, inda ya
bayyana cewar tun bayan da yarinyar tayi
korafi a ranar Juma’a aka kama wadanda akezargi
Wata makwafciyarsu ce ta kai korafi wajen jami’an tsaro, ta ce yarinyar ta kai mata koke, bayan da aka binciki yarinyar sai ta tabbatar da hakan, tare da cewar kusan shekaru biyu
kenan suna yin lalata da ita.
” Inji Daniel
To Allah Ya Kyauta Zamuso Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Mummunan Al’amari Dayake Faruwa Nayiwa Yara Kanana Fyade, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.